Wani bam da aka dasa a ya tashi a wajen Haramin Sayyida Zainabul Kubra dake ƙasar Syria.
Kafar yaɗa labarai ta cikin gida SANA ta bayyana cewa Mutum 6 ne suka rasa rayukansu, inda wasu mutum 23 suka tsira da raunuka sakamakon wannan harin ta'addanci.
An dasa bam ɗin ne a jikin babur a titin Kou Sudan a wajen Haramin na Sayyida Zainab (A.S).
Jami'an ƴan sanda da hukumomin dake da alhakin kulawa da lamarin sun garzaya inda lamarin ya faru inda suka ɗauki masu raunuka da shahidai zuwa asibiti a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar a shafin ta na Telegram.
Wannan harin ta'addanci ya auku ne daidai lokacin da miliyoyin al'ummar Musulmi ke gabatar da tarukan tunawa da kisan Imam Husain (A.S).
A irin wannan lokaci al'umma kanyi cincirindo a Haramin na Sayyida Zainab domin gudanar da juyayin Ashura.
Wannan hari dai shine na biyu a Haramin na Sayyida Zainab a cikin mako guda, an kai harin farko a ranar talata inda mutum biyu suka samu raunuka.
Zuwa yanzu dai babu wata ƴan ta'adda da ta ɗauki alhakin kai wannan harin na ranar Alhamis.
Ƙungiyoyin ta'addanci irinsu Da'ish,ISIS sun saba kai irin wannan hare-haren kuma su ayyana alhakin kai harin kamar yadda suka yi a shekarar 2017 inda suka kawo hari suka shahadantar da mutum 40.
0 Comments