- Freedom Fighters Ng
Tayar wata motar bus mai dauke da mutum 33 ta fashe inda hakan yasa motar tayi mummunan hadari tare da kamawa da wuta.
Wani dan sanda mai suna Sunil Kadasne ya bayyana wa manewa labarai cewa "Tabbas motar na dauke da mutum 33 a lokacin da hadarin ya auku, da misalin karfe 1:30 na dare a ranar asabar a babban titin Buldhana dake jihar Maharashtra".
"Mutum takwas sun tsira da rayukansu daga cikin mutum 33 inda aka garzaya da su asibiti".
Ita dai wannan mota ta taso ne daga Nagpur zuwa Pune ta biyo ta kan babban titin Samruddhi, daga faruwar hadarin tankin motar ya kama da wuta.
Mafi yawan wadanda suka mutu sun mutu ne sakamakon konewa da wutar da ta kama motar.
Mataimakin babban ministan Maharashtra Devendra Fadnavis shima ya tabbatar da mutuwar mutum 25 da kuma mutum 8 masu jinya, ya tabbatar da hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Shima dai babban ministan Maharashtra Eknath Shinde da kuma Firaministan Indiya Narendra Modi duk sun wallafa sakon tausaya wa tare da jajantawa a shafukansu na Twitter, kuma sun bayyana cewa zasu baiwa iyalan wadanda suka mutu tallafin rupee 700,000 wanda yayi daidai da dalar Amurka $8,500.
Narendra Modi ya ce " Ina addu'a tare da tunawa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu, ina yima wadanda suka samu raunuka fatan warkewa da wuri".
0 Comments