Rubutawa: Aliyu Samba
Idan aka ce wahada Islamiyya, shin me ma ake nufi?
* Shin tana nufin a sauka a dawo kan mazhaba guda daya ta addini a watsar da ragowar?
* Ko kuwa tana nufin a dauki abubuwan da dukkan mazahabobi suka hadu akai a tattara su tare da watsar da inda mazhabobin suka sassaba dan samar da sabuwar mazhaba da za a tafi akai wanda ta saba da wadda ake kai daban-daban a baya?
* Ko kuwa Wahada Islamiyya bai da alaka da banbance-banbancen mazhabobi, yana nufin hadin kan musulmi daga dukkannin mazhabobi, tare da banbance-banbancen ra’ayoyi da fahimtocin dake tsakanin su?
A kokarin da masu yaki da hadafin tabbatar da wahadar musulmi suke yi, sukan bijiro da shubuhar cewa ana nufin tabbata a kan wata mazhaba guda daya ne dan a rusa ragowar mazhabobi.
Saidai ko kusa Wahada Islamiyya bata da wannan ma’ana ko wannan hadafi, hakazalika ba ta nufin cewa a dauko abubuwan da aka hadu akai a tattara su a samar da sabuwar mazhaba tare da watsar da wuraren da aka sassaba. A zahiri ma hakan ya saba da hankali, kuma abu ne wanda bazai taba yiwuwa ba.
Wahada Islamiyya na nufin musulmi su hadu akan igiyar Allah guda daya da hana makiya addinin tasiri wajen kokarin cutar da addinin. A matsayin mu na musulmi, munyi tarayya a wani abu wanda zai iya zama tushen assasa hadin kai tsakanin mu. Dukkan musulmi suna bautawa Allah SWT, kuma dukkan musulmi sun hadu akan imani da Annabtar Annabi Muhammad ﷺ. Al’qur’ani shine littafin shari’ar da dukkan musulmi suka hadu akai, kuma ka’aba itace al-kiblar dukkan musulmi. Dukkan Musulmi suna zuwa aikin Hajji, kuma suna gudanar da shi tare, su yi dukkan rukunan hajji tare kuma a tsari da salo iri daya. Suna sallatar salloli 5 a kowacce rana, suna azumi a dukkan ramadan. Suna samar da iyali da kuma tarayya a cikin kasuwanci da cinikayya, suna samar da yara ta hanya daya, kuma suna binne mamatan su idan sun mutu. Idan aka dauke kananan al’amura da ba wadancan na sama ba, zamu ga cewa musulmi duka sunyi tarayya a wajen aikata su da imani da su.
Hakazalika, musulmi suna da alami iri daya a duniya, suna da al’ada guda daya da suka hadu akan ta, sannan suna da wayewa iri daya wacca take mai tsawon tarihi sama da shekara 1400.
Haduwar musulmi akan yadda suke kallon duniya, al’ada, wayewa, imani, da kuma ibada abubuwa ne da zasu iya tabbatar da wahada islamiyya wanda zai kara tabbatar wa da musulunci izza da buwaya.
Kwarai kuwa, hakan mai tabbata ne domin musulunci ya shinfida wata ka’ida, kamar yadda Al’qur’ani ya ambata cewa musulmi yan uwa juna ne, kuma akwai hakkoki da kowa yake da shi akan dan uwan sa. Menene yasa musulmi baza suyi amfani da wadannan tarin abubuwa da Allah ya azurta su da shi ba a cikin musulunci?
Wahada Islamiyya bata nufin cewa kowa ya jingine mataki na farko da na biyu na akidar s, haka kuma baya nufin musulmi su dena tattaunawa da bahasi tare da rubuta littafai akan manyan matakai na addini da suke da sabani akai.
Abinda kawai ake buri da fatan tabbatarwa a wahada islamiyya shine musulmi su toshe kofar kowacce irin mummunar baraka, a nisanci zagi da tuhumar juna, tozarta juna, cin zarafin juna, ko kuma cutar da juna. Sannan kuma su tabbata a manhajin da musulunci ya shardanta wanda aka shimfida dan gayyato wadanda ba musulmi ba ma su karbi addini.
“Ku yi kira zuwa ga tafarkin Allah cikin hikima da kyakyawan wa’azi, sannan ku yi mujadala da su ta hanya mafi kyau…..(Sura ta 16: Aya ta 125)
Akwai al’amarin da yake dauke da dukkan wani sirri na tabbatar wahadar Musulmi a duniya gaba daya, ba komai bane face al’amarin Ghadir khum wanda falsafar dake tattare da shi tun aukuwar sa, shine tabbatar da wahada Islamiyya, da kuma wanzuwar buwaya da izzar addinin Musulunci.
Ku biyo ni a rubutu na gaba mai taken
“Ghadir Khum: Sirrin tabbatar Wahada Islamiyya (II)”
~Aliyu Samba
5th July, 2023
0 Comments