Hakika akwai masana da ma'abuta gwagwarmaya daga KIRISTOCI da fitattun masana a duniya da suka yi bayanin yadda waki'ar ASHURA ta musu tasiri da yadda suke kallonta ga tsakure daga hakan:-
1 Marigayi Nelson Mandela yace:"Na shafe a yari, a wani dare na yanke shawarar in mika wuya ta hanyar sanya hannu a kan takardun yarjeniyoyin da gwamnati ta gindaya mini.Amma kawai sai na tuna tuna da Husaini da waki'ar Karbala.Sau kawai hakan ya ba nu kwarin gwiwa in tsaya a kan abin da yake shi ne gaskiya da ceton al'umma,sai kawai na fasa."
2.Thomas Caryle wani fitaccen Masanin Tarihin Kasar Scotland kuma gawurtaccen Marubuci yace:"Babban darasin da muka koya daga waki'ar Karbala shi ne Imam Husaini (as) da Sahabbansa mutane ne masu tsagwaron imani da Allah.Sun bayyana cewa,karfin jama'a ba shi da tasiri idan ana hamayya tsakanin gaskiya da karya.
Nasarar Husaini duk da cewa,su 'yan tsiraru ne,ta ba ni mamaki.
3.Edward G.Brown,Farfesa a sashen harshen Larabci da nazarce-nazarce a Jami'ar Cambridge Yana cewa:"Tunawa da filin da jini ya kwarara na Karbala,inda jikan Manzon Allah (s) ya fadi,aka azabtar da shi da kishirwa da kuma kewaye shi da gawarwakin 'yan uwansa wadanda aka karkashe,ya zamanto a kowanne lokaci tun da abun ya faru,yana tayar da bakin ciki da tashin hankali ko da kuwa a zaman lafiya da kwanciyar hankali ne.Hakan kuma Yana kawar da firgici da tsoron mutuwa."
4.Mahatama Ghandi (Shugaban Siyasa da addinin Indiya) yace:"Daga Husaini na koyi yadda Zan sami nasara a lokacin da ake zalunta ta."
5.Rabindranatha Tagore mawaqi mashhuri kuma cewa ya Yi:" sadaukar da kan Husaini ya nuna 'yantar da ruhi.Domin a rayar da adalci da gaskiya,maimakon karfin soji ko na makamai,za a iya samun nasara ta hanyar sadaukar da rayuka,daidai yadda Imam Husaini ya yi."
6.Charles Diskens kuma Marubuci ne dan Kasar Ingila ya rubuta cewa:"Idan Husaini ya yi yaki domin son Duniya ne,to idan haka ne ni ban fahimci hikimar dalilin da zai da 'yar uwarsa da matarsa da 'ya'yansa da za su raka shi ba.
Abin da hankali zai iya dauka shi ne cewa,ya bayar da rayuwarsa ne domin daukakar addinin Musulunci tsantsa."
7.Antoine Bara wata fitacciyar Marubuciya ce 'yar Kasar Labnan a sadda take fashin baki a kan sadaukarwar Imam Husaini (as) Yana cewa:"Babu wani yaki a Tarihin Dan Adam na da da yanzu da yake koyar da darussa kamar shahadar Husaini a yakin Karbala."(tsakuren daga littafin Husaini in Christian ideology).
8.Dr.K.Sheldrake ya rubuta cewa:"Daga wadannan gwarazan mabiya,maza da Mata sun sani sarai cewa rundunar makiyan da suka kewaye su ba su da tausayi.Husaini ya fuskance su da 'yan tsirarun mabiyansa,ba don yana da tabbacin samun nasara ba,ba domin neman girma ko daukaka ba,ba domin neman mukami ko Dukiya ba,amma sai don sadaukar da rai madaukakiya,kuma kowane mabiyinsa ya fuskanci shahada madaukakiya ba tare da nadama ba."
9.Dr.Radha Krishna ya rubuta cewa:"Duk da cewa Imam Husaini ya bayar da rayuwarsa shekaru aru-aru da suka wuce,amma shahadarsa ta mamaye zukatan al'umma har a yau din nan."
10.Mahatma Gandi ya rubuta cewa:"Imamina shi ne ci gaban addinin Musulunci bai dogara a kan amfani da takobin mabiyansa ba,amma ya dogara ne a kan Husaini,wanda shi babban waliyi ne."
11.Shi kuma Nehru ya bayyana sadaukar Imam Husaini (as) a yayin da yake cewa:"Sadaukar da kan Imam Husaini ba ta mabiya Shi'a ba ce,ta dukkanin kungiyoyi da al'ummu ne,wanda wani misali ne na turbar gaskiya."
12.Dokta Rajendra Prasad ya rubuta cewa:"Sadaukarwar da kan Imam Husaini ba ta takaita ba ga wata kasa kadai ba,amma wani gadajjen matsayi na 'yar uwantakar dukkan al'umma duniya ne."
13.Swami Shankaracarya ya bayyana cewa:"sadaukar da ran Imam Husaini ne ya sa addinin Musulunci ya ci gaba da rayuwa,in da bai yi haka ba da babu wani mutum daya a wannan duniyar da zai amsa sunan Musulmi.
14.Miss Sarojini Naidu ta rubuta cewa:"Ina taya al'ummar Musulmi murnar cewa,daga cikinsu ne aka sami Imam Husaini wanda dukkanin al'umma ke girmamawa."
Za mu ci gaba insha Allahu.
ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU
daga Yusuf Kabir.
09063281016.
15.Simon Ockley (1678-1720) Farfesan Larabci a Jami'ar Cambridge ya rubuta cewa:"Sai Imam Husaini ya hau dokinsa ya dauki Alkur'ani ya baje shi a gabansa ya tafi wurin mutanen,ya gayyace su zuwa abin da ya doru a kan su."
16.Ignaz Goldziher (1850-1921),Fitaccen Masani Dan Kasar Hungry ya rubuta cewa:"Tun daga ranar bakin cikin Karbala,tarihin al'ummar Musulmi ya ci gaba a matsayin damuwa da kuntatawa.Ana bayyana hakan ne a cikin wakoki da rubuce da suka shafi shahada,wadanda suka jibinci mazhabar Shi'a na musamman,da wadanda suka shafi tarurrukan Shi'a a farkon watan Muharram,wanda ake kebe goma ga wata a matsayin ranar bukukuwa juyayin waki'ar Karbala.Ana tunawa da abubuwan da suka auku a siffofin wasan kwaikwayo.Ranakun bukukuwanmu sune tarurrukan juyayi."
17.Edward Gibbon (1737-1794),wanda ake Wanda ake dauka a matsayin fitaccen mai ilimin Tarihin Ingila a lokacin da ya rubuta
cewa:"A shekaru masu nisa da garuruwa,waki'ar kashe Husaini za ta zaburar da tausayin mai karatun da yake cikin nutsuwa."
18.Shi kuma wani fitaccen manazarcin harkokin gabas ta tsakiya da ake Kira Peter J.Chelkowski Farfesa ne a kan nazarin harkokin Yankin gabas ta tsakiya a Jami'ar New York ya rubuta cewa:"Husaini ya fito daga Makka tare da iyalansa,da Kuna Tawagar mabiya 70.Amma a filin karbala,Khalifa Yazeed ya sa aka yi musu kawanya.Duk da cewa sun amince babu Nasarar,Husaini ya ki yarda ya yi masa mubaya'a.Bayan rundunar makiyan sun kewaye su Husaini da mabiyansa sun zauna babu ruwan sha tsawon kwanaki 10 a cikin saharar Karbala.Daga karshe,Husaini da manyan mabiyansa daga yara na cikin Iyalansa da mabiyansa aka karkashe su da Harbin kibiyoyi da takubban Sojojin Yazid.Aka kame matansa da sauran 'ya'yansa a matsayin firsunonin yaki a ka kaiwa Yazid a Damaskus.
19.Wani fitaccen mai ilimin Tarihin Abu Reyhan Al-Biruni ya fadi cewa:"daga nan sai aka cinnawa haimominsu wuta,aka kuma tattaka gawarwakinsu da kofaton dawaki.Babu wani a Tarihin bil'adama da ya dandanar irin wannan Bala'in.
20.Robet Durey (1835-1889),Manjo Janar ne na Sojan Bangladesh ya rubuta cewa:"Husaini yana da fa mai suna Abdullahi,Dan Shekara daya ko watanni da haihuwa.Ya raka Mahaifinsa a wannan waki'ar Da kukansa ya taba zuciyar Husaini (saboda kishirwa) sai ya dauki jinjirin a hannunsa ya yi kuka.A wannan lokacin,sai kaifin kibiyar makiya ta Huda makoshin jinjirin ya rasu a hannun Mahaifinsa.Husaini ya ajiye gawar jinjirin a kasa,yana cesa: Innalillahi wa Inna ilahir raji'un!
Ya Allah! Ka ba ni karfin zuciyar daukar wannan Bala'in."
21.Sir William Muir (1819-1905),Masani kuma babban jami'in da ya rike Sakataren harkokin wajen kasar Indiya da kuma babban Gwamnan Lardin Arewa maso yamma ya rubuta cewa:"Waki'ar Karbala ba kawai ta canza makomar khalifanci ba,har ma da al'ummar Annabi Muhammad (s) lokaci bayan lokaci mai tsawon da khalifanci ya kare."(Daga Littafin Annals of the Early Caliphate,London,1883 page 441-2).
- Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU
Na Yusuf Kabir.
kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.
Za mu ci gaba insha Allahu.
0 Comments