A wata sanarwa da ta fitar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tayi Allah wadai da yagawa tare da kona Qur'ani a gaban masallaci a kasar Sweden.
Hizbullah ta bayyana cewa dai hukumomin kasar suna da hannu a wannan aika aikar, tunda har suka bada damar yin wannan mummunan aiki duk da sanin abinda zasu aikata.
"Lalllai bazamu lamunci cigaba da cin mutuncin Qur'ani da ake yi a wannan kasa ta Sweden da sauran wurare a fadin duniya ba, kuma yazama dole Gwamnatin Sweden ta dakatar da wannan mummunan aiki, a daina fakewa da sunan 'yancin fadin albarkacin baki ana cin mutuncin Qur'ani".
" Muna kira ga hukumomi, kungiyoyi da Gwamnatocin kasashen larabawa da musulmi su dauki mataki kan wadannan kasashe da faruwar irin wannan aika".
0 Comments