Manyan Masanan Nukiliyar Isra'ila Na Barazanar Aje Aiki A Ƙoƙarin Goyon Bayan Masu Zanga-zanga.

 


Wasu manyan masana nukiliyar haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun yi barazanar ajiye aiki domin nuna goyon baya ga masu zanga zanagar adawa da ƙudurin sauya fasalin dokoki.


Kafar yaɗa labarai ta Israeli Channel 13 ta ruwaito cewa jami'ai da yawa daga wannan sashen na nukiliyar ƙasar suna yunƙurin ajiye aikinsu domin dafa ma masu zanga-zangar. 


Rahoton ya bayyana cewa waɗannan masana dai sune ke da alhakin cigabantar da sashen nukiliya na haramtacciyar ƙasar.


Rahoton ya ƙara da cewa babu wani shirin ɗaukar matakin bai ɗaya daga masanan, sai dai kowanne daga cikinsu yana tunanin ɗaukar matakin ƙashin kansa.


Tun farkon wannan shekarar ta 2023 ne dai ake ta fama da zanga-zangar ta adawa da ƙudurin sauya fasalin dokoki a haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila, a makon da ya gabata a ranar 24 ga watan Yuli, majalisar ƙasar ta amince da ƙudurin farko, saidai yarda da wannan ƙuduri, ya ƙara ta'azzara al'amarin zanga-zangar.


A ranar 22 ga watan Yuli, sojoji dubu goma (10,000) suka ayyana dakatar da aikin sakai da suke yi, wajen daƙile masu zanga-zangar a wajen wani taron manema labarai da suka gudanar a Herzliya,


A bangaren jam'iyyun ƙasar masu adawa da sauyin dokokin sun bayyana damuwa dangane da lamarin inda suka bayyana hakan a matsayin mulkin kama karya da Firaminista Netanyahu ke yima jagoranci, sun bayyana wannan a matsayin abinda zai kawo karshen demokradiyya a ƙasar.

Post a Comment

0 Comments