Juyin Imamu Husaini (as) daga Alkur'ani
Hakika juyin Imamu Husaini (as) ya kasance ya Samo asali ne daga Alkur'ani mai girma da kuma Hadisan Manzon Allah (s).Akwai ayoyi da daman gaske da suka bayyana wajibcin yin Umarni da abu mai kyau da kuma hani da mummuna.Allah
Dan haka wadannan ayoyin da muka ambata a sama kadan sun ishe mu zamantowa hujja dangane da juyin Imamu Husaini (as) daga cikin Alkur'ani.
Bugu da kari,mu kalli gaba dayan sakon Musulunci tun daga kan Annabawa da Manzanni dukkaninsu an aiko su ne domin su canza mutane daga hanya karkatacciya zuwa tafarki madaidaici.Don haka shi Imam Husaini (as) juyinsa ci gaban aikata sakon annabawa da Manzannin Allah (as)..
Juyin Imamu Husaini (as) a cikin Hadisan Manzon Allah (s).
Amma dangane da juyin Imamu Husaini (as) a cikin Hadisai kuwa,za mu ga cewa,Imam ya bayyana hujjar fitarsa daga wani Shararren Hadisi da ya rawaito daga Manzon Allah (s) a yayin da shi Imam (as) yake cewa:"Wanda ya ga Shugaba azzalumi mai halasta abunda Allah ya haramta,mai haramta abunda Allah ya halasta,Mai yin mu'amala da bayin Allah cikin sabo,to sai wanda ya ga Shugaban nan bai Yi fafutikar canza Shugaban nan da aiki ko magana ba,to Allah zai sanya shi makoma daya a ranar Alkiyama."(Littafin Umami wal Muluk na Dabari)
Fitatten Malamin nan Shaikh Kamaluddeen bn Dalhat yana cewa:"Hakika Kisan Husaini abu ne da yake sanya zubar hawaye daga idanuwa,yake tayar da damuwar zuciya,yake tsirar da bakin ciki a zukatan da suke da imani wannan duk a Sakamakon keta alfarmar zuriyar Annabi Muhammadu (s) da aka yi ne.Wannan duk fa suna sane da cewa,iyalan Annabi Muhammad (s) ne suka kashe tattare da lalata dukkanin gabobin jikinsu da kofatun dawakai."(Littafin Madalibul Su'al fi manaqibi Alil-Rasul page 261).Ga Hadisan da suka bayyanar da juyin Imamu Husaini (as):-
1.Manzon Allah (s) yana cewa:"Jibrilu ya tashi daga gare ni ya bayyana mini cewa Husaini za a kashe shi a gefen Kogin Furat,sai yace bari na nuna maka kasar da za a kashe a cikinta,sai ya debo kasar ya bani ita,sai ya zamanto ban iya hakuri ba sai da na Yi kuka."(Mu'ujamil Kabeer vol 3,page 105).
2.Daga Anas bn Harisata yana cewa:"Na ji Manzon Allah (s) yace:"Da sannu za a kashe Dana wannan (ya nuna Husaini) wanda ya riski lokacin ya taimaka masa." (Littafin Zaka'irul Ukba page 250). An rawaito cewa Ana's bn Harisata ya je Karbala tare aka kashe shi da Imamu Husaini (as)."(Littafin Kifayatul Dalib 386).
3.Daga Ibn Abbas Manzon Allah (s) yana cewa:"Jibrilu ya bayyana mini cewa za a kashe Dana Husaini."(Littafin Majma'ul zawa'id vol 9,page 194).
4.Daga Ummu Fadal ta ce:Manzon Allah (s) ya fadi mini a sadda Husaini yana kan cinyarsa:"Hakika Jibrilu ya bayyana mini cewa da sannu al'ummata za ta kashe Husaini."(Kanzul Ummal vol 12 page 123).
5.Hashim ya bayyana cewa:"Hakika Amiril Muminina (as) a sadda ya je Siffaini ya wuce ta Karbala sai ibn Abbas yace:Shin kasan wanne muhalli ne wannan?Sai nace:a'a,sai yace:"da a ce kasan wannan muhallin wannene da sai ka Yi kuka kuka mai tsanani."(Littafin Maqtalil Husaini na Kawarizimiy vol 1, page 162).
7.Daga Asbag bn Nabatata yace:"Mun kasance tattare da Ali bn Abu Dalib sai muka wuce Karbala,sai Ali (as) yace:"A nan ne ababen hawansu za su tsaya,a Nan ne za a zubar da jine-nansu wasu samari ne daga iyalan Muhammad sammai da kassai za su Yi musu kuka."(Littafin Sawa'iqul Muhrika page 192).
8.Daga Imamu Ali (as) yana cewa:"da sannu za a yiwa Husaini kisan gilla,na San bigiren da za a a kashe shi a kusa da Kogi biyu."(Littafin Nurul Absar page 221).
9.A sadda aka zagaye Imamu Husaini (as) a Karbala,ya yi tambaya yace:"Ya ya sunan muhallin nan?"Sai aka ce masa:"Karbala."Sai yace:"Annabi (s) ya yi gaskiya:"Tabbas Karbin-wa-bala'in ce"(Fusulil muhimma page 188).
10.Daga Ibn Shahari-Ashuub yace:"A sadda aka kashe Husaini na kasance a wajen Ummus Salama sai tace:"Sun kashe shi??!!Allah ya cika gidajensu da kabarurrukansu da wuta"Sannan sai ta fadi a sume."(Kifayatus Dalib page 399).
11.daga Ummu Salama tace:"Na ji Aljanu suna kuka a kan kashe Husaini." (Siyaru a'alamul nubala'i vol 4,page 428).
12.Daga Ummus Salama tace:"A sadda aka kashe Husaini bn Ali an Mana ruwa Kamar na jini a kan gidajenmu,kuma an bani labarin haka ta faru a Khurasan,Sham da Kufa."
13.Daga Abi Kital Yana cewa:"Hakika sama ta yi duhu a ranar da aka kashe Husaini har taurari suka bayyana da Rana."(Littafin Ansabul Ashraaf vol 2,page 505).
Littafai 10 da suka bayyana Manzon Allah (s) ya Yi bayanin juyin Imamu Husaini (as).
Fitaccen Malamin Shi'ar nan Allama Aminiy a cikin littafin "Siratuna wa sunnatina"ya bayyana wurare 10 Wanda Manzon Allah (s) ya yi bayanin Juyin Imamu Husaini (as) kashe da za a Yi.Ga bayanan Littafan kamar haka:-
1.Kukansa bayan an haifi Imamu Husaini (as).(A duba Zaka'irul Ukba page 119).
2.Juyayinsa a Radu'a.(a duba Fusulil muhimma page 154).
3.Bayaninsa a muhallin ra'asus sanati.(a duba Maqatalil Husaini Shaheed page vol 1,page 163).
4.Juyayinsa a Gidan Ummus Salama bayan Mala'ika Jibrilu ya bashi labarin abunda zai faru ga Imamu Husaini (as).(A duba Ibn Asakir a tarihinsa)
5.juyayinsa a Gidan Ummus Salama a karo na biyu (Haidami a Majma'ul zawa'id 9,page 189).
6.Juyayinsa a Gidan Ummus Salama bayan Mala'ikan Ruwa ya ziyarce shi.(Musnadi Ahmad 3/242).
7.Juyayinsa a Gidan Nana A'isha (Jauharatil kalam page 118).
8.Juyayinsa a dakin Sayyida Zainab bnt Jahash (Haisamiy a Majma'ul zawa'id 9/188.
9.Juyayinsa a Gidan Imamu Ali (as).(Hafeez Kawarizimiy)
10.Juyayinsa a cikin gungun Sahabbai.(Dabarani a Mu'ujamil Kabeer).
- Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ''ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU''
Daga Yusuf Kabir.
09063281016.
kabiruyusuf533@gmail.com
Za mu ci gaba insha Allahu.
0 Comments