MUSLIM BN AUSAJA' A FILIN KARBALA

 




Wannan fitaccen Jarumi daya daga gwarazan da suka yiwa addinin Musulunci hidima.Zaki ne wajen jarumta yana daya daga cikin Sahabban da suka Manzon Allah (s) ya kuma rawaito Hadisai daga gare shi.Ya kasance cikin fitattun Sahabban da suka hadu da Imam Ali (as) sannan suka Mika masa rayuwarsu wajen kariya.Ya halarci dukkanin yakokin Siffaini,Jamal,Naharwan Wanda Imam Ali (as) ya Yi.

Bayan Imam Husaini (as) yanayi ya tsananta a gare shi ya bar garin Madina zuwa Makka daga nan ya nufi hanyar Kufa,Muslim bn Ausaja'i ya kasance cikin 'yan gaba-gaban Mika masa mubaya'arsu.Bugu da Kari ya tattarawa Imam Husaini (as) mabiya da hidimtawa ta hanyar dukiya.

Hakika Muslmin bn Ausaja'i ya fuskanci takura,tsanani barazanar rasa rai domin bayar da kariya ga Ahalul Baiti (as) domin ya halarci Karbala domin bayar da kariya ga Imam Husaini (as) da rundunarsa.

Alkaluman Tarihi sun rubuta cewa a daren goma ga Almuharram Imam Husaini (as) ya nemi Sahabbansa su sulale cikin dare domin su tsira da rayukansu su kyale shi a falalen dajin Karbala Muslim yana daya daga cikin wadanda suka nuna za su kare Imam Husaini (as) da rayukansu domin kuwa yace da Imam Husaini (as):"Ina rantsuwa da Allah da ace da ace za a kashe ni sannan a qona ni,sannan a barbadar da tokar a cikin iska,a aikata mini haka sau 70,tabbas bazan barka ba,domin kuwa abinda za a mini kisa ne guda daya sai kuma dawwama cikin ni'ima har abada."(Littafin Manaqib v 4, page 99).

Sannan yace da Imam Husaini (as):"Yanzu idan muka barka da wand uzuri za mu gabatar a gaban Allah?! Wallahi ba za mu barka ba....Zan yi yaki har sai na karya mashina,zai yi yaki matukar takobina tana hannuna ba Zan taba barinka ba,zan rika jifarsu da duwatsu ba zan barka ba har in bar Duniya. 

Bayan an fara fito-na-fito an kasa samun a bangaren Yazidawa Wanda zai tunkare shi,ya kashe Yazidawa masu yawan gaske sai ya zamanto suka rika harbinsa da kibiya,masu da duwatsu har ya fado daga kan dokinsa.A sadda ya fado Imam Husaini (as) da Habibu bn Muzahir sun je wajenshi sai Imam Husaini (as) yace da shi:"Rahamar Allah ta tabbata a gare ka ya Muslim sannan ya karanta ayar (Faminhum man qada nahbahu wa minhum man yuntazar wama baddalu tabdima) (Ahazab 23).

Sannan Imam Husaini (as) ya masa bushara da Aljanna.

Hakika Muslim bn Ausaja'i (rta) ya kasance cikin jajirtattun Sahabban Imamu Husaini (as) da suka sadaukar da rayuwarsu a Karbala.

3.Bayanin Imamu Husaini (as) Daga Alkur'ani da Hadisai ga Musulmin da ba 'yan Shi'a ba.

Wane sirrin ne yake tattare da Imamu Husaini (as) har ya zamanto ya mallaki zukatan ma'abuta 'yanci a Duniya duk da shi ba Sarkin wata Masarauta ba ne ba?

Imam Husaini (as) ya zamanto maudhu'in tattaunawa ga dukkanin mutane da wadanda suka San 'yan adamtaka.Tarihi da girman Imamu Husaini (as) dimbin mutane sun yi rubutu a kan hakan da suka hada da Musulmi Sunni da Shi'a,Kiristoci,Yahudawa,Buzawa,Kai hatta wadanda ba su Yi riko da wani addini ba sun yi magana a kan Imamu Husaini (as).

Hakika fitattun Marubuta ana jiya da yau sun rubuta Littafai,Makaloli a kan Imamu Husaini (as) da juyin juya halin da ya gabatar.Duniya ta shaidi hazaka da shuhura da daukakar fitaccen Marubuci Farfesa Sayyid Abdul'ilah shi ma ya yi rubutu a kan Imamu Husaini (as) ya kuma bayyana matsayinsa da irin sadaukarwar da ya yiwa Tarihin Dan adam.Farfesa Sayyid Abdul'ilah ya kasance fitaccen Lakcara da ya koyar a Jami'oin mabambanta a Duniya kamar Iraki,Yeme, Aljeriya dss.

- Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ''ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU
Na Yusuf Kabir.
kabiruyusuf533@gmail. com

Za mu ci gaba insha Allahu.

Post a Comment

0 Comments