- Freedom Fighters Ng
Majalisar Dinkin Duniya, ta sake nuna damuwa game da rikicin Sudan, wanda ta ce yana da ci gaba da haifar da hijirar jama’ar kasar zuwa kasashe makobta.
Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce dauki ba dadin da sassan da ba sa ga maciji da juna ke yi a kasar Sudan, na ta’azzara matsalar raba al’ummun kasar da muhallan su.
Mista Dujarric ya ce MDD ta damu matuka da karuwar wannan adadi, inda alkaluman hukumar dake lura da bakin haure ko IOM, ke nuna cewa a makon da ya gabata, kusan mutane 200,000 ne suka kauracewa muhallan su a cikin kasar ta Sudan sakamakon yakin dake daidaita kasar.
Ya ce matakan shawo kan yakin kasar Sudan na tattare da manyan kalubaloli.
Yanzu haka dai watanni 3 ke nan, tun bayan barkewar yaki a Sudan, kuma tuni yakin ya raba al’ummar kasar sama da miliyan 2.6 da matsugunan su.
Game da karuwar adadin masu tserewa daga kasar kuwa, hukumar lura da ’yan gudun hijira ta MDD, ta ce ya zuwa yanzu, adadin masu tserewa ta kan iyakokin Sudan zuwa kasashe makwafta ya kai kimanin mutum 730,000.
0 Comments