Isma'il Magaji shugaban ƙungiyar ƴan sakai ta ƴan banga ya bayyana ma manema labarai cewa wasu mahara sun kai hari a garin Kangon Garaci, dake gundumar Ɗangulbi a yankin ƙaramar hukumar mulki ta maru dake jihar Zamfara.
Ƴan bangan sun tabbatar da mutuwar mutum 34 wanda a ciki har da sojojin Najeriya 7.
Yayinda yake zantawa da manema labarai wani mazaunin garin da aka kai harin ya bayyana cewa mutanen garin nasu 27 ne aka kashe sai wasu sojojin Najeriya guda 7 wanda ya cika lissafin mutum 34.
A zantawarsa ta wayar tarho da jaridar Daily Post Malam Usman Garaci, ya bayyana cewa maharan sun kawo harin ne da misalin karfe 4 na daren ranar Litinin, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi, kafin jami'an tsaron sojin Najeriya su kawo masu ɗauki.
Bayan waɗanda suka mutu dai akwai masu raunuka da dama.
0 Comments