Wannan ganawar shugaban ƙasar Koriya Ta Arewa Shugaba Kim da ministan tsaron ƙasar Rasha itace ganawa ta farko tun bayan annobar Covid-19.
Shugaba Kim da Shoighu sun tattauna akan alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da ta shafi harkokin tsaro da kuma ganin makamai (Weapons Exhibition) da suka haɗa da makamai masu linzami.
Tattaunawar da ta faru tsakanin shuwagabannin biyu takasance muhimmiya domin bunƙasa harkokin makamai.
Shugaba Kim ya zagaya da Shoighu ya nuna mashi sabbin kayan yaƙi. Kamar yadda aka gani cikin hotuna, ciki harda makamai masu linzami da sababbin jiragen yaƙi marasa matuƙa.
Shoighu ya baiwa shugaba Kim na Koriya ta Arewa wasiƙa rubutacciya daga shugaba Vladimir Putin na Rasha, shugaba Kim ya miƙa godiyar sa ga shugaba Putin a bisa aiko da wakilai da yayi domin tattaunawa da Ministan tsaron ƙasar Koriya ta Arewa Kang Sun Nam.
Ziyarar Minista Shoighu dai itace ziyara ta farko da jami'in wata ƙasar waje ya kai birnin Pyongyang a cikin shekaru uku da suka gabata, wannan ziyarar dai tazo ne a lokacin da Koriya ta Arewa ke bikin tunawa da shekaru 70 da tsaida yaƙin Koriya na shekarar 1950 zuwa 1953.
Hakanan tawagar wakilai daga ƙasar China sun kai ziyara ƙasar domin halartar wannan biki.
0 Comments