- Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Shaikh Zakzaky (H) yace “Sun yi niyyar za su yi ma Nijeriya irin yadda suka ma Somalia, yau Somalia shekaru kusan 30 sam babu gwamnati, zubargada ne kawai ake zaune, saboda haka za a je a debi arzikin ne kawai tunda ba gwamnati. To sun ce za su ma Nijeriya irin haka, ya zama yamutsi ne kawai, babu hukuma, sai yamusti don hakan ya fi saukin diban arziki. Kuma duk inda suke zuwa diban arziki haka suke yi.”
Shaikh Zakzaky ya yi bayani dalla-dalla a kan yadda Faransa ta haddasa rigima a Jamhuriyar Afirka ta Kudu, saboda tana son diban Dimond. Ya kuma kawo kissar yadda Amurka da Faransa suke gogoriyon neman Zinare a Mali, wanda ta kai ma ga sun rusa kasar. “Zinaren Mali da kuma Uranium din Niger, har an ce Faransa yanzu haka da Uranium din Niger take ba kasarta wutar lantarki, alhali ita Niger din bata da wutar Lantarki.”
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) har ila yau, ya yi bitan wata hira da Tsohon Gwamnan Arewa Maso Yamma, Alhaji Usaman Faroqu ya yi inda yace bayan da aka gama yaki, sai Ingila da Amurka suka zo, suka ce suna so a basu izini ‘liaising’ ya zama su ne za su debi ma’adinan karkashin kasa na Arewa maso yammacin Nijeriya. Aka ce masa shi yanzu a matsayinsa na gwamna, ya sa hannu a kan an basu ‘liaising’ din cewa duk ma’adanan da ke karkashin kasa a wannan yankin nasu ne. Amma yace shi kuma yace a’a, ba zai saka hannu ba, sai dai in za a hada da Rasha, saboda da muka yi yaki Ingila da Amurka sun hana mu makamai, rasha ta taimake mu da jiragen saman yaki aka kawo karshen yakin nan, amma ku Ingila da Amurka kun ki sayar mana, saboda haka yanzu sai dai a ce har da su. Sai suka ce a’a, su Ingila da Amurka kawai za a ba. Sai yace ba zai sa hannu ba a matsayinsa na Gwamna.”
Jagora yace, Alhaji Usaman ya bayyana cewa: “Daga baya Amabasadon Rasha a Nijeria yace masa, ka san abin da yasa su kadai suke so ku ba wannan lasi din? saboda kuna da ‘uranium’ ne, idan da za a
0 Comments