Shekaru uku da suka gabata a rana mai kamar ta yau 22 ga watan july, azzalumar hukumar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Janar Buhari ta afkama masu muzaharar kiran a saki jagoran harkar Musulunci Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a sakatariyar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Gamayyar jami'an tsaron Najeriya ne sukayi haɗin gwuiwa wajen afkama masu muzaharar, inda suka kashe mutum goma nan take daga cikin masu muzaharar, sai dai cikin mutum goma da suka kashe gawar mutum shida kawai aka samu, sauran gawarwakin mutum huɗun sun ɗauke su sun tafi dasu, anyi jana'izar mutum shidan kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Bayan kisa kuma, mutane da dama ne suka samu raunuka, wasu ankaisu asibiti, wasu kuma sun tafi gida da raunuka.
Sai dai jami'an tsaron basu ƙyale waɗanda aka kai asibiti ba, domin kuwa sun bi har asibitin Gwagwalada sun kwashe su, a daidai lokacin da aka fara baiwa wasu kulawa, wasu kuwa ko mota basu sauka ba jami'an tsaron suka kwashe su cikin jini suka kai Hedkwatar ƴan sandan birnin tarayya kafin su maida su wajen ƴan sandan SARS.
Daga cikin waɗanda suka kwaso a asibitin, akwai masu munanan raunuka akwai mai karaya a cinya a dalilin harbin bindiga, mai harbi a baki, masu harbi a ciki wanda har hanjinsa ya fito waje, da wasu munanan raunuka, kuma an ajesu anan tsawon lokaci ba tare da kulawar likita ba, har mutum uku daga ciki sukayi shahada anan ofishin ƴan sandan SARS, wasu kuma har sai da ƙafar su ta fara tsutsotsi idan ka kalla sau ɗaya ba zaka sake kallo ba.
Bayan masu raunuka kuma an kama mutane da yawa tsawon kwanaki uku, tunda daga ranar Litinin har zuwa ranar Alhamis.
A ranar 4 ga watan 10 na shekarar 2022, jami'an tsaro sun bada gawarwakin mutum uku daga cikin gawarwakin waɗanda suka kwashe.
Ƴan uwan da aka tsare da masu raunuka adadin su yakai mutum sittin (60) mata 6 maza 54, bayan shafe tsawon watanni a Cell ɗin ƴan sandan SARS batare da zuwa kotu ba, daga ƙarshe an kai su kotu, bayan zaman farko kotu ta bada umarnin a kaisu gidan kaso a zaman kotun na biyu a ranar 10 ga watan 12 na shekarar 2019.
An kai maza gidan yarin Kuje, mata kuma gidan yarin Suleja, sai dai gidan yarin kuje sun ƙi karɓar wasu daga cikin masu raunuka, haka yasa aka maida su asibitin ƴan sanda, daga bisani alƙali ya baiwa masu ranuka da ke asibitin ƴan sandan beli su uku, daga bisani kuma alƙalin ya sake baiwa mata beli su 6 a ranar 17 ga watan 3 na shekarar 2020.
A lokacin wannan waƙi'a jami'an ƴan sandan sun kashe wani babban jami'insu mai muƙamin mataimakin kwamishina, da wani ma'aikacin gidan talabijin na Channels TV, sai dai sun ɗora alhakin kisan waɗannan mutane akan ƴan uwan da suka kama, suna tuhumar su da aikata wannan kisa da wasu laifuka har goma sha biyar (15), duk da cewa basu da hujja ko ɗaya, amma dai hakan suke cigaba da tsare su bisa zalunci.
Har yanzu dai sauran ƴan uwan suna tsare a gidan yarin Kuje, dake Abuja.
A shekarar da ta gabata sojojin Najeriya sun kashe ɗaya daga cikin ƴan uwan da ke tsare a gidan yarin na kuje a lokacin da wasu mahara suka kai hari gidan yarin da sunan ta'addanci, sojoji ne suka harbe ɗan uwan mai suna Jibril Usman Sarki, yayinda yake ƙoƙarin komawa cikin gidan yarin bayan tafiyar maharan, sakamakon fitowa da sukayi lokacin da maharan suka fasa gidan yarin.
Ana nan dai ana cigaba da yima waɗannan ƴan uwa shari'ar zalunci.
- Ibn Tukur Almizan
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments