SHIMFIDA
Hakika karnoni suna wucewa lokaci bayan lokaci a yayin da mutanen da suka zauna labarinsu da ayyukansu masu kyau da marassa kyau ke wanzuwa kamar yadda kissar Annabi Musa (as) da Fir'auna ta wanzu.Sai dai lamarin Imamu Husaini (as) da waki'ar Ashura ya zamanto na daban a Tarihi.Waki'ar Karbala ta zamanto babbar Jami'ar da ta fitar da Jaruman da raunanan Duniya ke fakewa a cikin inuwarsu.
Waki'ar Ashura ba ta zamanto wacce ta takaita ga wata kasa,ko yare,ko yanki,ko kabila,ko jinsi ba,tabbas haskenta ya keta dukkanin iyakoki da nahiyoyi.
Daga nan za mu tabbatar da cewa Hakika Imamu Husaini (as) ya sadaukar da kansa,iyalansa,Sahabbansa domin tseratar da addinin Musulunci Wanda Allah ya aiko Kakansa Annabi Muhammad (s),ya kuma tabbata da takobin Mahaifinsa Imamu Ali (as) da dukiyar Kakarsa Sayyida Khadijat bnt Khuwailid (as).
Hakika Imamu Husaini (as) ya zamanto wanda sadaukarsa ta kara tonawa azzaluman Mahukuntan Banu Umayya asiri.Sadaukarwarsa ta zamanto wacce ta shuka Bishiyoyin da bayin Allah suka fake a karkashinsu domin samun ni'imtacciyar rayuwa.Imam (as) ya bayyana shahararriyar maganarsa mai tsadar gaske a yayin da yake cewa:"Idan addinin Muhammad ba zai tabbabata ba sai da kashe ni ya ku takubba ku yi raga-raga da jikina."
WANENE IMAMU HUSAINI (AS)?
A bisa ingantattun ruwayoyi an haifi Imamu Husaini (as) ne a rana ta uku ga Sha'aban shekara ta hudu bayan hijirar Manzon Allah (s) zuwa Madina.(littafin ikbalili a'amal:689).
A wata ruwayar kuma da ban ta bayyana cewa daya daga cikin matan Aljanna da ake kira La'iyya ita ce ta karbi haihuwar Imamu Husaini (as).
Bugu da kari fitaccen Malamin Shi'ar nan da ake Kira Shaikh Dusiy ya bayyana cewa:"haihuwar Husaini ta kasance ranar Alhamis uku ga watan Sha'aban."(Littafin Ifshadil mufeed 2/27).
Za mu ci gaba insha Allahu.
© Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ''ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU''
daga Yusuf Kabir.
kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.
0 Comments