Akwai ayoyi masu yawan gaske da suka bayyana daraja da matsayin Imamu Husaini (as) ga wasu daga ciki:-
1.Imamu Husaini (as) daya daga cikin mutane biyar da aka saukar da ayar "Tadhir" a kan su.(Littafin Mu'ujamil Sagir 1,176 H,177,Sunani Tirmiziy 5,page 699 ha 3871,Siyaru a'alamul nubala'i hadisi 3787,Bugyatul Dalib vol 6,page 3580).
Wannan ayar ta bayyana cewa Imamu Husaini (as) Ma'asumi ne da nissin Alkur'ani mai girma.
2.Imamu Husaini (as) daya daga cikin wadanda aka saukar da ayar Mubahala a kan su ne,hakan ya faru ne a sadda Kiristocin Najran suka suka so yin Mubahala da Manzon Allah (s). (A duba Littafin Nurul Absar na Shaikh Mu'umin bn Hasanil Shiblanji page 45).
3.Imamu Husaini (as) daya daga cikin wadanda Ahalul Baiti ne wanda aka wajabta kaunarsu.Daga Ibn Abbas Yana cewa:"A sadda aka saukar da ayar "Ka ce musu bani tambayarku wata lada face ku so iyalan gidana."
Wadannan tsakure kenan daga ayoyin da suka sauka a kan Imamu Husaini (as).
Ayoyin nan da muka ambata ba mun dan tsakuro ne.
IMAMU HUSAINI (AS) A CIKIN HADISAI
Kamar yadda muka ambata a sama kadan dangane da ayoyin da suka sauka akan Imamu Husaini,Manzon Allah,Sayyida Zahra,da yayansa Imamu Hasan (as).A yanzu insha Allahu za mu kawo Hadisan da Manzon Allah (s) ya fadi a kan Imamu Husaini (as) saboda girman matsayinsa:-
1.Manzon Allah (s) yana cewa a sadda ya lullube Imam Hasan,Imamu Husaini,Sayyida Zahra da Imamu Ali da mayafi:"Ya Allah!Wadannan sune iyalan gidana,kuma kebantattuna,ya Allah ka tafiyar da datti daga gare su ka tsarkake su tsarkakewa,sai Ummus Salama tace:Shin Ina tattare da su ya Rasululllahi?Sai yace:"Hakika ke kina tattare da alkairi."(Littafin Sunani Tirmiziy vol 5,page 699).
2.Manzon Allah (s) yana cewa:"Yana cewa:"An kira 'ya'yan Haruna Shabran da Shubairu,Hakika na kira 'ya'yana Hasan da Husaini da irin sunan da Haruna ya Kira 'ya'yansa."(Littafin Mu'ujamil Kabir vol 3,page 97,Kanzul Ummal vol 12,page 117,Musnadi Ahamad bn Hambal vol 2,page 159,Hadisi na 769).
3.Manzon Allah (s) yana cewa:"Hasan da Husaini suna ne daga cikin sunayen Aljanna Larabawa ba su taba sanyawa 'ya'yansu a Jahiliyya ba."(Littafin Sawa'iqul Muhrika page 192).
4.daga Rafi'i daga Babansa Manzon Allah (s) yana cewa:"Na ga Manzon Allah (s) ya yi kiran sallah a kunnen Husaini a sadda aka Fatima ta haife shi."(Mustadarak a sahihaini vol 3,page 179)
5.Manzon Allah (s) yana cewa:"Hakika Hasan da Husaini su ne farin ciki a Duniya."(Littafin Isaba fi tamyizis Sahaba vol 1,page,332).
6.Manzon Allah (s) yana cewa:"Mafi alkairin mazajenku shi ne Ali bn Abu Dalib,mafi alkairin Samarinku su ne Hasan da Husaini,mafi alkairin matanku ita ce Fatima bnt Muhammad."(Tarikus Dimashqa vol 14,page 129 Hadisi 3419).
7.Daga Ja'afar bn Muhammad daga Babansa yana cewa:"Hasan da Husaini da Abdullahi bn Ja'afar suna kanana,babu yara kanana da suka yi mubaya'a sai su."(Littafin Iqidil farid vol 4,page 351,Tarikus Dimashqa vol 14,page 180 h:3517).
8.Manzon Allah (s) yana cewa:"Hasan da Husaini Shugabannine sune ke rike da Jagoranci ko ba su ba ne ba."(Muntakabil Ma'asumin na Ahamad Furati).
9.Daga Abu huraira yana cewa:"Mun dawo daga wata tafiya,Manzon Allah (s) ya sanya harshensa a bakin Hasan da Husaini har sai da suka kishirwar da suke ji ta kauce daga gare su."(Littafin Tahzibul Tahazeeb na ibn hajar vol 2,page 298).
10.Manzon Allah (s) yana cewa akan Hasan da Husaini:"Hakika su ruhin raina ne masu faranta mini:"(Sahhil bukari kitabul adab)
11.Manzon Allah (s) yana cewa:"Hakika Hasan da Husaini sune farin ciki na a wannan al'ummar."(Kasa'isul nisa'i page 37).
12.Manzon Allah (s) yana cewa:"Ya Allah!Ka sani Hakika Hasan da Husaini 'yan Aljanna ne."(Littafin Zaka'irul Ukba page 130).
14.Manzon Allah (s) yana cewa:"wanda yake So na to ya so wadannan biyun (sai ya nuna Hasan da Husaini) (Sunanil baihaki vol 2,page 263).
15.Manzon Allah (s) yana cewa:"Ya Allah ka shaida Ina son su,ka so su,ka so wanda yake son su."(kanzil Ummal vol 7,page 107)
16.Manzon Allah (s) Yana cewa:"Hasan da Husaini Shuwagabanni samarin Aljanna ne."(Tirmiziy vol 2,page 306).
.
17.Manzon Allah (s) Yana cewa:"Hasan da Husaini su ne Shuwagabannin samarin aljanna,amma Mahaifinsu ya fi su matsayi."(ibn Majah babin falalar Sahabbai).
18.Manzon Allah (s) yana cewa:"Husaini daga ni yake,nima daga shi nike,Allah ya so wanda ya so Husaini, Husaini da ne daga 'ya'yana."(Tirmiziy vol 2,page 307).
19.daga Imamu Ali (as),Manzon Allah (s) yana cewa:"Da sannu za a kashe Husaini,nasan kasar da za a kashe shi a ita kusa da Koguna biyu."(Kanzul ummal vol 7,page 110).
20.Manzon Allah (s) yana cewa:"Za a kashe Dana Husain a gefen kogin furat,Wanda ya riske shi ya taimaka masa."(Nurul Absar na Shaikh Mu'umin bn Hasanil Shiblanji)..
Za mu ci gaba insha Allahu.
- Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ''ASHURA A MAHANGAR KIRISTOCI DA MASANA A JIYA DA YAU
na Yusuf Kabir.
kabiruyusuf533@gmail.com
09063281016.
0 Comments