Ministan Sadarwa na Kongo Thierry Moungalla ya ce babu kanshin gaskiya game da rahotannin da ke cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Denis Sassou Nguesso ranar Lahadi.
Gwamnatin kasar Kongo Brazzaville ta musanta rahotannin da ake watsawa a soshiyal midiya cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Denis Sassou Nguesso ranar Lahadi.
Ministan Sadarwa na kasar Thierry Moungalla ya wallafa sako a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter da ke cewa ya kamata ya yi “gaggawar” karyata rahotannin juyin mulkin domin kuwa na “kanzon-kurege”.
“Wasu bayanai na karya sun nuna cewa wasu manyan abubuwa suna faruwa a Brazzaville. Gwamnati tana musanta wannan labari na karya,” in ji shi.
“Muna masu tabbatar wa jama'a cewa komai na tafiya cikin kwanciyar hankali a (Kongo), kuma mutane na harkokinsu kamar yadda suka saba.”
© Saliadeen Sicey
0 Comments