Gwamnatin Paris na shirin afkama Nijar domin ta cigaba da jibge dakarun sojojin ta a ƙasashen ƙungiyar ECOWAS mabanbanta dake yankin Afirka ta yamma, cewar gwamnatin sojin Nijar
Alaƙa dai tana ƙara tsami a tsakanin Nijar da Faransa tun bayan juyin mulkin da sojojin sukayi a cikin watan Yuli.
A wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin ɗin ƙasar Kanal Amadou Abdramane ya bayyana cewa " Faransa na cigaba da jibge dakaru a ƙasashen mambobin ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma (ECOWAS) mabanbanta, duk a yunƙurin afkama ƙasar mu ta Nijar, kuma wannan haɗaka ce tsakanin Faransa da wannan ƙungiyar ta ECOWAS" kamar yadda jaridar AFP ta ruwaito a ranar asabar ɗin da ta gabata.
Kanal Amadou Abdramane dai shine mai magana da yawun gwamnatin sojin Nijar.
Tun bayan faruwar wannan juyin mulki dai ƙungiyar ECOWAS take ta barazanar sanya ƙarfin soji domin ƙwace mulki daga hannun sabuwar gwamnatin sojin ƙasar, hakanan kuma jami'an gwamnatin Faransa mabanbanta sunyi ta furucin cewa Faransa zata goyi bayan ɗaukar matakin soji a ƙasar ta Nijar, sunyi waɗannan kalamai a lokuta daban daban, wannan na ƙara tabbatar da batun da Kanal Amadou Abdramane ya yi na cewa haɗaka ce tsakanin Faransa da ECOWAS.
A kwanan baya dai Firaministan gwamnatin sojin ƙasar ta Nijar Ali Lamine Zeine ya bayyana cewa basa goyon bayan dukkanin wani matakin soji da ECOWAS keson ɗauka, kuma sabuwar gwamnatin su tana ƙoƙarin tattaunawa da ƙungiyar ta ECOWAS.
Sai dai kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron a lokacin da yake jawabi a taron G20 da aka gudanar a makon da ya gabata a ƙasar Indiya, ya bayyana cewa tunda ƙasar ta Nijar bata buƙatar Faransa a ƙasar bazai ƙara tura dakaru ƙasar ba, sai dai idan tsohon shugaba Bazoum ne ya nemi hakan.
Ya ƙara da cewa ba Nijar bace ƙasa ta farko da Faransa ta janye sojojin ta daga ciki ba, domin kuwa ko a farkon shekarar nan mun janye sojojin mu daga Burkina Faso da Mali sakamakon rashin daidaito da gwamnatocin sojin kasashen biyu.
0 Comments