Wani nazari da aka yi akan farashin danyen mai a duniya Wanda aka yi a yammacin ranar Alhamis 14 ga watan satumba, ya nuna cewa danyen mai na Brent ya haura zuwa dala 94 kan kowace ganga, sakamakon karuwar matsalan karancin kayan aiki. Wannan tashin gwauron zabin ya zo ne bayan rahotonnin baya-bayan nan da ke nuna tasirin raguwar hako mai a kasashen Saudiyya da Rasha, wadanda suka taimaka wajen hauhawar farashin Mai a 'yan makonnin da suka gabata.
Abun sha'awa danyen mai Brent ya Kai matsayin mafi girman farashi tun farkon shekarar 2023. A baya dai Nairametrics ta ruwaito cewa Saudiyya da Rasha sun yanke shawarar tsawaita rage hako man da suke hakowa har zuwa karshen shekarar 2023, a lokacin sanarwar farko a watan yulin da ya gabata danyen mai na Brent baya haura dala 76 a kowace ganga.
Imamu Mahadi Umar kaita.
FFNG Hausa.
0 Comments