Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayar da umarnin dakatar da shugabannin sashen koyon harshen faransanci da na sashen koyon harshen kasar sin, a Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi a jihar Nan take take saboda rashin zuwa aiki.
Haka zalika ma'aikatar ta amince da nada Umar Akilu Sabo a matsayin shugaban kwalejin koyon harshen faransanci, sai aka nada Isyaku Umar Abdullahi a matsayin shugaban kwalejin koyon harshen kasar sin dake Kwankwaso.
Wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar a ranar Litinin yace "Shugabannin da aka dakatar ba sa cikin makarantun a lokacin da tawagar jami'an tsaro suka Kai ziyarar gani da ido a ranar litinin domin Sanya ido kan yadda za'a fara sabon zangon karatun. sanarwar tace "Tawagar sa idon a karkashin babbar sakatariyar ma'aikatar Hajiya Kubra Imam ta gano cewa ba a ba wa daliban kwalejin biyu abinci a daren lahadi ba, Kuma ba a shirya musu abun Karin kumallo ba da zasuci ranar litinin har zuwa lokacin ziyarar.
Daga karshe kwamishinan ya bayyana a cikin sanarwarsa cewa "shugabannin makarantun biyu su Maida hankali wajen ganin sunyi namijin kokari wajen kyautata muhallin makarantun da kyautatawa daliban.
Karshen rahoton kenan
©️ Imamu Mahadi Umar kaita
Freedom firgters NG Hausa.
0 Comments