Wani jirgin fasinja mai lamba A320 wanda ya tashi daga Novosibirsk yayi saukar gaggawa da safiyar yau Talata, yayin da jirgin ya buƙaci sauka an bashi umarnin sauka a wani filin saukar gaggawa dake Novosibirsk, sai dai kuma anyi rashin Sa'a inda jirgin ya faɗo kafin zuwa filin.
Jaridar Al'ahed ta bayyana cewa jirgin yayi saukar gaggawa a wani fili nisan kilomita 180km daga babban filin tashin jirage na ƙasa da ƙasa dake Novosibirsk, inda dama can ne jirgin zaije.
A cikin wannan jirgi dai akwai sama da mutum 170, ciki harda ƙananan yara 23, rahoton farko na bayan faruwar lamarin ya nuna cewa babu wani daga cikin fasinjoji ko ma'aikatan jirgin da ya rasa ranshi ko ya samu mummunan rauni.
Hukumomin sun bayyana cewa jirgin bai fashe ba, kuma bai kama da wuta ba, wannan dalilin ne ya taƙaita lamarin, anyi nasarar kwashe mutane lafiya daga cikin jirgin.
A wasu hotuna da suka yaɗu a zaurukan Telegram, anga yadda akayi nasarar fitar da mutane daga jirgin, harma anga wasu fasinjojin a tsaye a gefe guda.
Gwamnan jihar Novosibirsk da Omsk sunyi alƙawarin taimakawa fasinjojin da dukkanin taimakon da suke buƙata sakamakon faruwar lamarin, wanda ya haɗa da sutura da kuma samar masu sa yadda zasu cigaba da wannan tafiya.
Itama hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar ta ƙaddamar da bincike kan faruwar lamarin.
https://mindlessslogan.com/zp33eru4?key=54c45af8a8cf77445807ff793b470a45
0 Comments