MASU HAKAR MA'ADINAI BA BISA KA'IDA BA NA ANFANI DA SHANU WAJEN JIGILAR ZINARE DAGA NEJA ZUWA KASAHEN MAKWABTA.

 



Gwamnan jihar Neja Muhammad Bago ne ya Fadi Hakan a ranar laraba inda ya bayyana cewa masu hakar ma'adinai da makiyaya ba bisa ka'ida ba na amfani da shanu wajen safarar zinare daga jihar Neja zuwa kasashen makwabta.


Akwai babbar matsalar rashin tsaro da ya addabi jihar a Yan kwanakin Nan, da yake jawabi a Wani babban taron manema Labarai na duniya da akai a Abuja, Gwamna Bago ya bayyana cewa jihar ta shirya kar6ar bakuncin taron koli na tattalin arzikin kasa na farko, Wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 24 da 25 ga watan oktoba, 2023 yace suna kokari na ganin sun kar6i wuraren da yan fashi suka mamaye a jihar. Yace taron koli na tattalin arzikin Green zai Sami halartar mahalarta Sama da 500 daga bangarori daban daban don tattaunawa don taimakawa wajen samar da mafita ga al'amurran da suka shafi lalata tsarin makamashi, tattalin arziki, sarrafa sharar gida, noma, samar da abinci, yawon shakatawa da ci gaban al'umma.


ya Kara da cewa jihar nada hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da Sojoji domin kawar da kasar Nijar daga masu aikata laifuka, jihar Neja dai ana tunanin itace jihar da tafi yawan makiyayan shanu a duniya.


Ya Kara nanata kudirin sa na ci gaba da bunkasa albarkatun kasa mai daraja ta hanyar anfani da sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki da wadata tare da dakile masu fasa gwabrin zinaren ba bisa ka'ida ba.


Imamu Mahadi Umar kaita

FFNG Hausa

Post a Comment

0 Comments