Shugaban kwamitin Task Force na jihar Taraba, janar Jeremiah Faransa (Rtd) ya koka kan yadda sama da mutane 20,000 ke da hannu wajen hako ma'adinai da sare itatuwa a jihar.
Yace Yan kasashen waje sama da 100 aka kama, ya Kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da Kuma masu kishin kasa a fadin jihar. Wani farmaki da tawagar da gwamnatin Taraba ta Kafa a sansanin masu hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba ta hana hako ma'adinai da sare itatuwa ba bisa ka'ida ba.
Bayan isar su rundunar ta gano wasu gidaje na wucin gadi da Kuma wasu bindigogi a hannun masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, da ake zargin ana amfani da su wajen yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan fashi da makami.
Karkashin umarnin gwamnan jihar ya bada izinin a kone dukkan wasu kaya da aka samu a wajen inda a take aka kona dukkan injuna da rumfuna dake wajen.
A cewar shugaban kwamitin binciken ya nuna cewa ayyukan hakar ma'adinai na zama babban hadari Kuma Yana taimakawa Yan fashi wajen gudanar da lamurransu.
® Imamu Mahadi Umar kaita
FFNG Hausa
0 Comments