Daga Aliyu Assufiy Algambiawiy
Ahlussunah sun tafi akan cewa, Cika ta Allah ce shi kadai, kiyayewa ga kuskure ta manzanni ce su kadai, wannan tasa duk abinda za ace yazo daga wajen waninsu, yana kasancewa ne tsakanin daidai da kuskure. Wannan ne dalili na farko da yasa a musulunci kafin izinar wata magana ana farawa ne da nassin Alqur’ani, domin shi kadai ne “La ya’atihil badili min baini yadaihi wala min khalfihi”, amma a sanda aka ce a je ga ruwayoyin hadisai, to ba shakka akwai buqatar karawa fitila haske, domin ba dukkan abin da aka rubuta cikin littafan hadisu suke ingatattu ba. Sau tari zaka samu hadisai a jere cikin littafi guda, qarqashin babi guda, amma kowannensu yana rushe dayansa, a tare da haka kuma a kallafawa kai i’itiqadi da su wanda hakan yayi nesa da hankali. A nan ma zamu bi mas’alar nan ta wafatin manzon Allah SAWA kamadda tazo cikin Littafin Abu Abdullahi Muhammad bn Isma’il bn ibrahim Al Bukhariy wanda aka fi sani da sahihul Bukhari. Alkamalu lillahi, hakika Bukhari ya kawo maganganun da suka sa dole duk mai kishin addinin musulunci musamman a yau da farmakin Kafirai da Mulhidai yayi yawa kansa, ya yi kyakyawan duba dan tsame tsaaba daga tsakuwa, domin muddin aka tafi akan haka, za a cigaba da rushe addinin ne daga cikinsa, Allah ya kiyaye.
Bukhari cikin Littafinsa Sahihul Bukhari yayi babi mai suna ” Babin Rashin lafiyar manzon Allah SAWA da wafatinsa kamadda yazo a hoton da ke kasan wannan post. A ciki ya kawo a hadisi mai lamba ta 4437 kamar haka:
حَدَّثَنَا أَبُو الْيَمَانِ أَخْبَرَنَا شُعَيْبٌ عَنِ الزُّهْرِيِّ قَالَ عُرْوَةُ بْنُ الزُّبَيْرِ إِنَّ عَائِشَةَ قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهْوَ صَحِيحٌ يَقُولُ: ((إِنَّهُ لَمْ يُقْبَضْ نَبِيٌّ قَطُّ حَتَّى يَرَى مَقْعَدَهُ مِنَ الْجَنَّةِ ثُمَّ يُحَيَّا أَوْ يُخَيَّرَ)). فَلَمَّا اشْتَكَى وَحَضَرَهُ الْقَبْضُ وَرَأْسُهُ عَلَى فَخِذِ عَائِشَةَ غُشِيَ عَلَيْهِ، فَلَمَّا أَفَاقَ شَخَصَ بَصَرُهُ نَحْوَ سَقْفِ الْبَيْتِ ثُمَّ قَالَ: ((اللَّهُمَّ فِي الرَّفِيقِ الأَعْلَى)). فَقُلْتُ إِذًا لاَ يُجَاوِرُنَا. فَعَرَفْتُ أَنَّهُ حَدِيثُهُ الَّذِي كَانَ يُحَدِّثُنَا وَهْوَ صَحِيحٌ.
(Isnadi….) Nana Aisha RTA tace: Annabi sawa ya kasance a sanda yake halin lafiyarsa lau yana cewa, babu wani Annabi da ake karbarsa face an nuna masa masaukinsa a aljannah, sai a bashi zabi na rayuwa ko ya mutu. Tace: Da annabi yayi rashin lafiya Ajalinsa yazo, yana kwance kansa na cinyata ya suma, yayin da ya farfado sai ya kafe ganinsa zuwa sama yana kallon rufin dakin, sannan yace: “Allahumma fi rafiqil a’ala”……….
Mu dauki wannan ruwaya mu gwadata da wadda ke bin ta hadisi mai lamba ta 4438 muji nan kuma me ya ruwaito:
حَدَّثَنَا مُحَمَّدٌ حَدَّثَنَا عَفَّانُ عَنْ صَخْرِ بْنِ جُوَيْرِيَةَ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ الْقَاسِمِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَائِشَةَ دَخَلَ عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ أَبِي بَكْرٍ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا مُسْنِدَتُهُ إِلَى صَدْرِي، وَمَعَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ سِوَاكٌ رَطْبٌ يَسْتَنُّ بِهِ، فَأَبَدَّهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَصَرَهُ، فَأَخَذْتُ السِّوَاكَ فَقَصَمْتُهُ وَنَفَضْتُهُ وَطَيَّبْتُهُ، ثُمَّ دَفَعْتُهُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَاسْتَنَّ بِهِ، فَمَا رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ اسْتَنَّ اسْتِنَانًا قَطُّ أَحْسَنَ مِنْهُ، فَمَا عَدَا أَنْ فَرَغَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَفَعَ يَدَهُ أَوْ إِصْبَعَهُ ثُمَّ قَالَ: ((فِي الرَّفِيقِ الأَعْلَى)). ثَلاَثًا ثُمَّ قَضَى، وَكَانَتْ تَقُولُ مَاتَ بَيْنَ حَاقِنَتِي وَذَاقِنَتِي.
(Isnadi……) Nana Aisha tace: Abdulrahman bn Abi bakr ya shigo min ina jingine da manzon Allah a kirjina, a hannun Abdulrahman akwai danyen asuwaki yana goge hakorinsa dashi, sai annabi ya kafawa asuwakin nan na Abdurrahman ido, Aisha tace: sai na karba daga hanunsa na taunashi, na kakkabeshi, na wanke shi, na bawa Annabi shi ya goge bakinsa dashi, ta cigaba da cewa: ban taba ganin annabi ya goge hakori gogawa mai kyau irin wannan ba, yana gama gogewa sai ya daga hannunsa ko yatsansa sannan ya ce “Firrafiqil Al’ala” sau 3. Sannan ya cika. Take cewa Annabi sawa ya cika ne tsakanin ruwan cukina da kirjina.
Idan mun gwada tsakanin hadisan nan 2 zamuga tufka da warwara mai girma a cikinta wadda ke tabbata dayan biyun hadisannan karyane domin ba ta yadda za a hade tsakaninsu.
•Ruwaya ta farko tana cewa an karbi Manzon Allah sawa kansa na kan cinyarta, ta biyu kuma an karbeshi kansa yana jingine kirjinta. Wannan kuwa bazai yiwu ba a ce hadisai 2 dinnan sun inganta saidai in sau 2 aka karbi ransa, domin lafuzan sun saba kuma duka daga maruwaici daya.
•Idan ta jingina annabi a kirjinta, to ba shakka kansa yana saman kanta domin an ruwaito ya fita tsayi, shin zai yiwu kuma a ce kansa yana cinyarta?
Asqalani yayi kokarin hade tsakanin wadanan ruwayoyi biyun a Fathul Bari Juzu’i na 7 Shafi na 808, inda yake cewa:
” Babu sabani a tsakanin wadannan ruwayoyi domin abinda hali yake nunawa, jawo Manzon Allah SAWA tayi daga cinyarta zuwa kirjinta….”
Wannan sabsada Tasa dole mu wajjahar da wasu tambayoyi da zasu bayyana mana shin hakan zai yiwu, kuma za a iya hade tsakanin hadisan:
1. Yaushe Nana Aisha ta zama mai karfin da Manzon Allah Yana sume ta iya jawoshi daga kan cinyarta zuwa kirjiinta Alhalin tana zaune, domin bukharin ya ruwaito cewa tace yayin da Annabi yayi shekaru, yayi teba, yayi jiki da wasu kalmomi marasa dadi kamar cewa baya iya ruku’u, kuma ya rage tsayin raka’o’in da yake?
2. Ruwayar cewa tayi Annabi ya suma kansa yana kan cinyarta, da ya farfado ya kafe idansa yana kallon rufin dakin (Sama) har ya cika, wannan ya nuna yana kishingide a rigingine kamadda ruwayar ta nuna. Saboda haka Bazai yiwu ace yana zauneba domin wanda za a ce idansa na kafe yana kallon sama to ba shakka a kwance yake, idan yana zaune saidai ya kalli bango ba sama ba. Yaya akai aka samu ruwayar cewa yayi wafati a kirjinta kuma?
3. Ko zaune mutum yake ya suma kwantar dashi ake saboda jinkai, tayaya za a ce a cikin sumansa kwance ta taada shi zaune?
4. Yana daga Amanar magana, iyar da ita yadda take, Idan yadda Ibn hajar yafada din hakane cewa ta tashe shi zaune, shin akwai amanar magana ga sauya waqi’i da cewa yayi wafati a cinyarta?
5. Yazo a wata ruwaya duk a shafi daya a cikin bukhari cewa tace yayi wafati kansa yana tsakanin ruwan cikina da kirjina, a wata kuma a cinyata, a wata kuma bayansa na jingine a kirjinta, shin sau 3 Aka karbeshi kenan?
6. Mu qaddara ingancin Ruwayar data zo a hadisi na 4437 cewa yayi wafati kansa cinyarta, zai zama ya rushe na 4440
حَدَّثَنَا مُعَلَّى بْنُ أَسَدٍ حَدَّثَنَا عَبْدُ الْعَزِيزِ بْنُ مُخْتَارٍ حَدَّثَنَا هِشَامُ بْنُ عُرْوَةَ عَنْ عَبَّادِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ الزُّبَيْرِ أَنَّ عَائِشَةَ أَخْبَرَتْهُ أَنَّهَا سَمِعَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَصْغَتْ إِلَيْهِ قَبْلَ أَنْ يَمُوتَ، وَهْوَ مُسْنِدٌ إِلَيَّ ظَهْرَهُ يَقُولُ: ((اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي، وَأَلْحِقْنِي بِالرَّفِيقِ)).
(Isnadi……..) Nana Aisha Tace taji annabi sawa kafin ya cika yana mai jingina min gadan bayansa yana cewa: Allahumagfirli, warhamniy wa alhiqniy birrafiq.
Da abinda bature ke cewa “And Vise Versa”. Shin ya kamata a cigaba da cewa dukkan abinda yanzo a bukhari sahihi ne tunda an gaza hade tsakanin sihahu 3?
Idan mukayi duba zamuga cewa muna da ruwayoyi ne guda 3 a jere ras cikin littafin bukhari wanda babu yadda za ayi a hade tsakanin su, saidai a tabbatar da daya a rushe ragowar, wanda hakan ke qara haska mana cewa lallai akwai lauje cikin nadi, magana ta gaskiya daya ce, dukkan hadisannan karya ne. Zan cigaba da dorawa a post na 2 insha Allah.
©Algambiawiy 21/10/2018
Twitter: @Algambiawiy
Email: sambaaliyu@yahoo.com
Gmail: algambiawiy@gmail.com
®Kwamitin wayar da kai na Mujamma’u Ashabil Kahfi warraqeem.
0 Comments