Daga - Mahadi Tukur Almizan
An ruwaito cewa anga wata tawagar sojojin Amurka na jigilar kayan soji daga ƙasar Iraqi zuwa ƙasar Syria.
Kayan da sojin suka kwashe sun haɗa da makamai da man fetur daga sansanonin sojin Amurka dake Iraqi zuwa Syria dake maƙotaka da ƙasar ta Iraqi.
Wata boyayyar majiya ta bayyana ma jaridar Al-Mayadeen cewa tawagar sojin tashiga gabashin ƙasar Syria ta iyakar Faysh Khabur, bayan sun fito daga yankin ƙurdawan Iraqi a sirrance a daren jiya Litinin.
A cikin ƴan watannin nan dai Amurka ke ta ƙara jibge sojojin ta a ƙasar ta Syria, duk da cewa hukumomin ƙasar sunyi ta fitowa suna ayyana wannan matakin na Amurka a matsayin haramtaccen motsi.
Ko a watan da ya gabata fadar tsaro ta Pentagon ta tura sojoji zuwa sansanonin sojin Amurka dake Deir Ezzor ta mashigar Al-Waleed Border dake tsakanin Iraqi da Syria.
Gamayyar motocin soji 50 suka shiga sansanonin sojin Amurka dake filayen ɗibar sinadarin Gas dake Koniko da Al-Omer oil a ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata.
Sai dai fadar Pentagon tace wai manufar ajiye waɗannan sojoji shine kare waɗannan muhallan ɗibar man daga faɗawa hannun ƴan ta'addan wahabiya na Da'esh wato ISIS.
Sai dai kuma hukumomin ƙasar Syria sun bayyana cewa ajiye waɗannan sojoji yana nufin maƙarƙashiya ga arziƙin ƙasar su, domin kuwa su ke da haƙƙin kare albarkatun ƙasar su, in ma bada kariyar ne.
Hukumomin ƙasar Syria da sun zargi Amurka da sace masu mai da yakai darajar dala biliyan 115.2
0 Comments