Daga- Mahadi Tukur Almizan
So dayawa mutane na son sauke bidiyoyin TikTok, sai dai basu buƙatar Watermark ɗin dake jikin bidiyoyin.
Menene Watermark;
Watermark a jikin bidiyoyin TikTok yana nufin logo da sunan TikTok da kuke gani a jikin bidiyoyin.
Watermark yana nufin dukkanin wata alama da ake ɗorama bidiyo dake alamta asalin inda aka ciro abu, ko kuma ayi abu, ana saka Watermark har a jikin takardun litattafai tayadda zakuga wani babban rubutu yayi dishi dishi a bayan rubutun dake jikin takardun, hakanan zakuga wasu Application na gyaran bidiyo, idan kayi aiki dasu suna barin sunan App ɗin a jikin bidiyon, kamar KineMaster Wadda ba premium ba.
Banner 320×50
A yau zanyi maku bayanin yadda zaku sauke bidiyoyin TikTok ba tare da suna da logon TikTok dake jikin bidiyoyin ba.
Da farko kashiga TikTok, idan kaga bidiyon da kakeson saukewa, saika taɓa alamar sharing, zakaga wajen copy link, saikayi copy ɗin link ɗin bidiyon.
Kamar haka 👇
Daga nan saika zo Kashiga wannan website ɗin ta wannan link ɗin 👉🏼https://ssstik.io/en kayi pasting link ɗin, idan yakawo bidiyon, saika taɓa alamar download, Shikenan zakaga bidiyon ya sauka babu Watermark.
0 Comments