TARIHIN MAZHABAR JA'AFARIYYA A TAKAICE (1).

 



Daga Siddiq Kabir

09063281016.


kabiruyusuf533@gmail.com


09063281016.

 Ganin muna cikin watan Mauludin Manzon Allah (s) da jikansa Imam Ja'afarus Sadiq (as).A daidai gabar nan muka ga dacewar sake bijiro da rubutun nan domin tunatarwa,Allah ya amfanar da mu bihakki Maulatana Zahra (as).


MATASHIYA


Asalin rubutun nan muqala ce da aka yi sati 13 a na bugawa a Jaridar Almizan a shafin MADUBI,an buga ne a tsakanin shekarar 2019.






Mamaki zai Iya zabare tunanin mutane da suke adawa da 'yan Shi'a saboda ire-iren aqidunsu da ibadunsu da suka bambanta a waxansu gavovi da na sauran Mutane;bayan kuma su suna gudanar da ibadunsu ne a qarqashin  Mazhabar Ja'afariyya wacce  ita ce farkon Mazhabar da ta samu a cikin da'irar  Addinin Musulumci. ka ga kuwa dole kowa a sami wadannan bambance-bambancen ko''?


 Ja'afariyya dai Itace zallar  haqiqannin koyarwar da Manzon Allah (s) ya yi a tsawon Shekaru 23  da ya xauka yana Da'awa.Hakan kuma ba zai zamanto wani abun musu da Wofantarwa ba Saboda Kasancewar Mu'assasinta shine Imam Ja'afar Sadiq  limami na 6 daga cikin Wasiyyai 12 da Littafan Ahalus-sunna wal jama'a suka kawo Hadisai baja-baja akansu.shi xan Gidan Manzon Allah (s) ne Wanda ya gaji Ilimi,ibada,kyauta,daga kakansa Annabi  Muhammad bn ABDULLAHI bn Abdulmuxxalib (as).Saboda haka ilimin gidansu ne ya cigaba da yaxawa Halitta domin su samu sa'ada a ryuwar yau  Duniya,da gobe lahira da muka tunkara gadan-gadan ta yadda za su jewa mahaliccinsu sun bauta masa da koyarwar littafin da ya saukar wa Manzonsa (s) da karantarwar Manzon ba ta waninsa ba!

 


MI YA SA AKE KIRANTA JA'AFARIYYA?




A na ce mata JA'AFARIYYA ne Saboda an jingina ta da limamin shiriya,madogarar Halitta a zamaninsa Imam Ja'afar bn Muhammad As-sadiq (as),amma tun daga kan Manzon Allah (s) har Imam Mahadi (AF) (wanda Hadisan da aka rawaito  akan bayyanar sa  ba za su gaza yawan waxanda aka Rawaito akan sallah da Azumi  ba) akan gwadaben koyarwar ta suka bautawa Allah (t) har suka qaura zuwa mahaliccinsu (ma'ana sun bi koyarwar Gidan Manzon Allah tsintsane ba ta wani gida ba)

Kamar yadda ake kiran  Mabiyan Imam malik bn ANAS da  'yan Malikiyya,ake kiran Mabiyan imam Shafi'i da 'yan Shafi'iyya,ake kiran Mabiyan imam Ahamad bn hambal da 'yan  Hambaliyya,ake kiran Mabiyan imam Abu Hanifa da 'yan hannafiyya waxanda waxannan sune mazhabobin Duniyar Ahalussuna wal jama'a guda 4 da suka yi qaurin suna (duk akwai waxansu da su ka narke koyarwar su ta valvalce aka wurgasu cikin kwandon Tarihi tun Xaruruwan Shekaru da suka gilma) to,haka ake kiran 'yan Shi'a Mabiyan Ahalul baiti (as) da 'yan Ja'afariyya.wacce itace Mazhabar 'yan Shi'a qwalli xaya tilo da suka duqufa wajen bautawa Allah (t) da ita.

 Wanda aka jingina Sunanta da na sa shine;Ja'afar xan  Muhammad Al-baqir xan  Ali bn Husaini (zainul Abidin),xan  HUSAINI bn Ali Dan Sayyida Fatima Zahra  (as) diyar Annabi Muhammad (s).wannan itace nasabarsa a taqaice kuma kai tsaye har ya zuwa Manzon Allah (s).

 




MI YA SA BA TA SHAHARA BA?



 Wannan ya farune a sakamakon yadda Azzaluman Mahukumta suke farautar Limaman 'yan Shi'a da mabiyansu domin su yanyankasu,haka ta sa ba su damar baje-kolin koyarsu ba da miqe qafa kamar yadda suke so.an hana su (limaman Shi'a) haxuwa da Jama'a,an yanke musu Duk hanyoyin da Kuxaxe za su isa wajensu,an yaxa farfagandodi marassa toshe ballantana Usuli akansu,rayuwarsu ta riqa tafiya ne a tsakanin gidajensu da kurkukun Sarakunan daular Banu umayya da Banil Abbas hakan ta sa Mazhabar Ahalul baiti (as) Ja'afariyya Sunanta,koyarwarta,bai wani dogon zango ba.a haka aka keto Xaruruwan Shekaru a haka kuma a ke cigaba da rayuwa har yanzu. Wannan ita ce taqaitacciyar shimfixa akan Mazhabar Ja'afariyya!yanzu kuma za mu koma batu akan imam Sadiq (as).


Za mu ci gaba insha Allahu.

Post a Comment

0 Comments