Wanene Shaikh Shaheed Ahmad Yaseen Wanda Ya Assasa Rundunar Hamas?

 



Daga Siddiq Kabir

Sunansa Ahmad Isma'il Yaseen,an haife shi a garin Jauzatil-Asqalani da ke lardin Gazza cikin kasar Palasdin.


Shaikh Ahmad Yaseen ya ta so cikin jarabawar rasuwar Mahaifinsa tun yana dan shekara 3 a duniya.Ya ta so ne yana maraya a sakamakon rasuwar Mahaifinsa a yayin da Mahaifiyarsa ce ta ci gaba da kula da  rayuwarsa.


Gwagwarmayarsa da karatunsa!



Shaikh Ahmad Yaseen ya yi karatu a Gazza daga bisani ya ci gaba da karatunsa a jami'ar Azhar da kasar Masar.A yayin da yake karatu a Masar kuma,ya tasirantu da fikirorin 'yan uwa Musulmi da ke Misra wanda Shaikh Hasanil Banna ya kafa da musu tarbiyya.


Yadda Isra'ila ta tsare a kurkuku.


Haramtacciyar Qasar Isra'ila ta kama Shaikh Ahmad Yaseen tare da tuhumarsa da ayyukan nuna kin jinin Yahudawa da kyamata su a cikin al'umma.Da wannan dalilin ne ta kama shi a shekarar 1983 ta tuhumar fafutikar kawar da Yahudawa a yankin,a shekarar 1985 kuma suka sake shi a yayin musayar Fursunoni da aka  aiwatar tsakanin 'Yan Hamas da Yahudawan Isra'ila.


A shekarar 1991 aka sake kama shi,a yayin da wata kotu a Isra'ila ta yanke masa hukuncin rai-da-rai,daga bisani dai Allah ya kubutar da shi daga hannunsu.


Shaikh Shaheed Ahmad Yaseen,Dr.Shaheed Abdulazeez Rantisi su  ne dai suka  kafa kungiyar Hamas da suke bayar da kariya ga kasar Palasdinu daga kisan kare dangin da Yahudawa suke yi a zirin Gazza.


Shahadarsa!

Yahudawa 'yan share-guri-zauna ne dai suka shahadantar da Ahmad Yaseen ta hanyar ruwan Bama-bamai a kan sa da 'yan rakiyarsa a sad da ya dawo daga masallaci bayan kare sallar Asubahi.

Post a Comment

0 Comments