HAIHUWAR SAYYIDA ZAINAB {S•A}

 



بسم الله الرحمن الرحيم

      اللهم صل على محمد وآل محمد


Haihuwarta:- An haifetane a ranar 5 gawatan Jimada Ulah shekara 5 bayan hijira 

Sunan mahaifinta Imam Aliyu bn Abiy-Dalib, Sunan mahaifiyarta Sayyida Faɗimatu bnt Muhammad {A•S}, Kakanta Annabi Muhammadurrasulillah bn Abdlhi {S•A•W•W). 


     SUNANTA

Cikakken sunanta Sayyida Zainab bnt Aliyu bn Abiɗalib {A}.


     LAƘABINTA

Ana yimata laƙubbah kamar haka:-

1-Assidiƙatul sugra   4-Al-Arifa

2-Aƙilah           5-Al-Kamilah

3-Aƙilatu bani hashim.


     ALKUNYARTA

Anayi mata alkunya da

1-Ummu Kulsum

2-Ummu Hassan

3-Zainabul kubra


     MIJINTA

Mijinta shine Abdullahi bn Ja'afar, kuma ya kasance shine wanda aka fara haihuwa a habasha lokacin hijira ana yimasa alkunya da Abu-Muhammad da kuma Abu-Ja'afar 


     ƳA'ƳANTA

Ta kasance tana da ƴa'ƴa 4

1-Muhammad 3-Aliyu

2-Aun      4-Ummu kulsum


     JARUMTARTA DA JURIYA DA HAKURINTA

Ta kasance jaruma ako'ina  akoda yaushe kuma tayi hakuri da rashin mahaifinta da ƴan uwanta musamman 

Imam Hussain {A•S} Ta nuna juriya da hakuri da jarumta. 


     IBADAH

Ta kasance mai yawan bauta ga Allah 

Sallah, Azumi, Karatun Al-Ƙur'an, Sadaƙa, Kyauta


Imam Hussaini yayi mata wasiya yace 

{Ya Zainab karki manta dani a nafilolinki a koda yaushe) 

Sannan yazo a ruwaya cewa Sayyida Zainab tana bauta ga Allah kamar yaddah babanta da mahaifiyarta. 


     WAFATIN SAYYIDA ZAINAB {A•S} 

Yazo a ruwaya cewa Sayyida tayi wafatine a ranar shabiyar ga watan Rajab bayan hijira da shekara 62 bayan shahadar ɗan uwanta da shekara 4 da wata 6 da kwanaki 5 an bizneshi a (Dimashq)  A birnin sham wanda yanzu shine siriya dalilin dayasa tayi wafati acan shine tayi tafiya tareda mijinta Abdullah bn Ja'afar zuwa sham saboda yanada lambu acan. 

Alokacin ne ta fara rashin lafiya wanda bata daɗeba tayi wafati.


   Aka binneta acan sannan tayi wafati tana mai kwaɗaitar da mutane akan daukar fansar Imam Hussain {A•S} 

     ALHAMDULILLAH•••


وصلى الله على محمد وآل محمد

By: Munasaba Committee Fudiyyah Funtua.

Post a Comment

0 Comments