Wani babban jami'in majalissar ɗinkin duniya ya bayyana akwai yiwuwar cututtuka zasu kashe ƙananan yara da yawa a Gaza fiye da adadin da hare haren Bama Baman da Isra'ila ke kaiwa Gaza ya kashe.
Mai magana da yaqin kwamitin kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF James Elder yayi kira da a gaggauta samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yayi gargaɗin ce indai har ba a dakatar da yaƙin ba, cututtuka da mace mace zai zarce adadin Yaran da hare haren Bama Baman Isra'ila ya kashe a yankin na Gaza.
James Elder yayi wannan kira ne a ranar Talatar da ta gabata inda ya wallafa a shafin UNICEF na kafar X wadda aka fi sani da Twitter a da " Ƙarancin ingantaccen ruwan, abinci da kayan tsaftace muhalli da jiki waɗanda tsagaita wuta ne kawai zai bada damar kawo agajin su, zai iya sabbaba mutuwar yara da yawa sakamakon cututtuka".
A halin yanzu dai alƙaluma sun bayyana cewa aƙalla Palasɗinawa dubu 20 ne suka rasa rayukansu a Gaza, inda ma'aikatar lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana cewa daga cikin wannan adadin Yara dubu 7 da ɗari bakwai ne suka rasa rayukansu, waɗanda haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila ta shahadantar.
A kwanakin dai wani rahoton na UNICEF ya bayyana cewa kusan dukkanin wasu wuraren wasan Yara da ke yankin na Gaza ya zama kufai sakamakon hare haren jiragen yaƙin Isra'ila.
Rahoton na UNICEF ya bayyana cewa " A halin yanzu Gaza ita ce guri mafi muni ga Yara a faɗin Duniya".
A halin yanzu dai yankin na Gaza na cikin matsanancin Takunkumin na hana ruwa, abinci, magani, da man fetur shiga Gaza, wanda ya jefa al'ummar Gaza aƙalla mutum Miliyan 2.3 cikin matsanancin hali.
0 Comments