A daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke tururuwa wajen nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu da dukkannin abinda suke iyawa, su kuwa wasu gurbatattun ƙasashen Musulmi taimakon Isra'ila suke.
Ƙasar Jordan ta kakkaɓo makaman da ƴan gwagwarmaya na Iraqi suka harba zuwa Isra'ila, kamar yadda kasar Saudi Arabia tayi a cikin watan Oktoba yayin da dakarun Ansarullah na Yemen suka harba makamai zuwa Isra'ila.
A ranar Juma'a 22 ga wannan wata na December ƴan gwagwarmaya na Iraqi suka fitar da sanarwa cewa su ke da alhakin harin da aka kai birnin Eliat dake kudancin Isra'ila, kuma wannan hari sun kai shi sakamakon hare haren da Isra'ila ke kaiwa kan al'ummar Palaɗinu.
A cikin sanarwar ƴan gwagwarmayar sun bayyana cewa domin mayar da martani dangane da kisan kiyashin da Isra'ila ke aiwatar wa ne kashe fararen hula, ƙananan yara da mata harma da tsofaffi a Gaza, mujahidan musulunci na Iraƙi sun hari Ummu al-Rashrash dake birnin Eliat da makamai.
🚨 The Islamic Resistance in Iraq struck a target in Umm al-Rashrash in Zionist occupied territory Eilat, with appropriate weapons 🇮🇶 pic.twitter.com/9oYWOKt6g0
— أبو سجاد الكربلائي | HST 🇮🇶 (@Twelver313) December 21, 2023
Kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun labarto cewa ƴan gwagwarmayar Iraqi sun kawo hari da jirgi maras matuƙi zuwa birnin kudancin Isra'ila, amma dakarun tsaron sararin samaniya na kasar Jordan sun yi nasarar kakkaɓo jirgin maras matuƙi.
Hakanan kafar yaɗa labarai ta Lebanon Al-Manar ta bayyana cewa Jordan ta baiwa Isra'ila kariya ta hanyar kakkaɓo jirgi maras matuƙi da mujahidan Iraqi suka harba zuwa Isra'ilar.
Sai dai rundunar sojin ta Jordan bata fitar da sanarwa dake tabbatar da wannan aika aika ba.
0 Comments