An samu shahidi da masu rauni.
✍️ Mahadi Tukur Almizan
Jirgin yaƙin Amurka ya kai hari shelkwatar (headquarter) rundunar ƴan gwagwarmayar Iraqi da ake kira PMU (Popular Mobilization Units) wadda da larabci ake kira "Quwwatu Hashad al-sha'abi" , wannan hari yayi sanadiyyar shahadar sojan rundunar 1 wasu 18 kuma sun samu raunuka.
Majiyoyin jami'an tsaro sun tabbatar ma kafar yaɗa labarai ta Shafaq News Agency cewa jirgin yaƙin na Amurka ya hari shelkwatar ta Hashad al-sha'abi dake Al-jazaer dake yankin Babel ta tsakiya.
Wata sanarwa da fadar mulkin Amurka White House ta fitar ta bayyana cewa Joe Biden ne da kansa ya bada umarnin kai harin a wurare uku wanda rundunar Kata'ib Hizbullah da wasu rundunoni masu alaƙa da ita suke aiki, musamman ayyuka da jirage marasa matuƙa.
Mayaƙan gwagwarmaya na Iraqi dai sun ƙaddamar da hare hare mabanbanta a Iraqi da Syria tun farkon Ɗufaanul AQsa domin nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu.
Ƴan gwagwarmaya sun bayyana cewa su na kai hare haren sansanonin Amurka ne saboda goyon bayan Isra'ila da take.
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments