Ban Nemi Netanyahu Ya Tsagaita Wuta Ba A Wayar Da Muka Yi - Joe Biden

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan


Duk da yawaitar kiraye kirayen al'umma, ƙasashe da ƙungiyoyi na neman Isra'ila ta  tsagaita wuta a Gaza, Amurka na cigaba da kaima Isra'ila tallafin makamai.


A ranar asabar ɗin da ta gabata 23 ga wannan wata na December, shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya bayyana ma manema labarai cewa shi bai nemi Netanyahu ya tsagaita wuta a Gaza ba a wayar da suka yi ta ƙarshe.


" 📞 Nayi doguwar waya da Netanyahu yau, kuma wayar ta sirri ce", a cewar Biden, amma dai "ban nemi ya tsagaita wuta a Gaza ba".


Fadar White House ta bayyana cewa Biden yayi waya da Netanyahu inda suka tattauna akan yaƙin na Gaza kan 'Objectives da kuma Phasing' na yaƙin.




Sai dai fadar ta White House ta bayyana cewa Biden ya ƙarfafa maganar tsananin buƙatar kare rayukan fararen hula da kuma masu ayyukan bada agaji, da kuma muhimmanci baiwa fararen hula damar zuwa muhalli mai tsaro, duk a cewar fadar ta White House.


Wannan kiran waya tsakanin Biden da Netanyahu ya biyo bayan kwana ɗaya da matakin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da yayi kira da a ƙara tallafin jin ƙai amma kuma kwamitin ya gaza wajen neman a gaggauta tsagaita wuta.


©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments