Dakarun Ansarullah Sun Ƙosa Su Yi Arangama Da Amurka - Muhammad al-Bakhiti.

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan

Wani babban jami'in Ansarullah ta Yemen ya bayyana cewa dakarun sojojin na Ansarullah sun ƙosa su fara arangama da dakarun Amurka A Red Sea.


"Saƙon mu zuwa ga maƙiya shine Dakarun Yemen sun ƙagara su tunkari maƙiya wato Amurka".


Jami'in na Ansarullah Muhammad al-Bakhiti yayi wannan kalaman ne a ranar juma'ar da ta gabata.


"Kamar yadda Yemen tayi nasara a yaƙin da tayi da ƙawancen Amurka, haka za tayi nasara a duk lokacin da aka Kawo mata hari". A cewar al-Bakhiti.


Amurka dai ta sanar da ƙaddamar da ƙawancen aikin baiwa jiragen ruwa na dakon kaya da dakarun Ansarullah ke kaima hari a Red Sea.


Sai dai a hukumance Ansarullah ta gargaɗi Amurka cewa "In har jiragen yaƙin Amurka suka hari Yemen to lallai suma zasu fuskanci hari, kuma Amurka tana sane da ƙarfin wannan matsayar ta Ansarullah".


Da yake magana akan ƙin shiga wannan ƙawance na Amurka wajen baiwa jiragen Isra'ila kariya da Saudi Arabia da ƙasar Dubai tayi al-Bakhiti ya bayyana wannan mataki da suka ɗauka a matsaya kyakkyawar matsaya.


Ya ƙara da cewa yaƙin Yemen a Red Sea kariyar kai ne amma zai iya canzawa anan gaba.

©️ Freedom Fighters Ng

A ranar Alhamis ƙungiyar ƴan gwagwarmayar ta Ansarullah ta fitar da sanarwar cewa dukkanin jiragen dakon kaya suna iya wuce wa ta Red Sea lafiya Ƙalau ba tare da fuskantar wata barazana ba, amma ban da jiragen Isra'ila ko kuma masu kai kaya haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila.

Post a Comment

0 Comments