ISRA'ILA ZATA BUƊE SABON SHAFI A YAƘIN TA DA HAMAS: Janye Sojojin Ƙasa Da Cigaba Da Kai Hare Hare Ta Sama

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta labarto a jiya asabar cewa Tel Aviv na shirye shiryen buɗe sabon babi a makonni masu zuwa, wannan sabon shafi zai kawo ƙarshen yaƙin sojojin ƙasa, inda kuma zasu cigaba da kai ƙazaman hare hare ta sama.


Kafar yaɗa labaran ta ƙara da cewa wannan sabon shafi ya ƙunshi " Kawo ƙarshen yaƙin ƙasa, rage yawan dakarun...".


A sabon shafin za su mayar da hankali wajen kai ƙazaman hare hare ta sama, samar da Buffer Zone kusa da bodar Gaza wadda zata haƙƙaƙar da burikan Isra'ila na mamaya.


Wannan rahoto na Isra'ila ya biyo bayan kwana ɗaya da janye dakarun rundunar 'Golani Brigade' na Isra'ila daga fagen daga, ita wannan runduna ta Golani Brigade ta karɓi wuta a hannun mayaƙan Qassam Brigade, Quds Brigade da sauran wasu rundunonin mayaƙan Palasɗinawa a Gaza.



Wani tsohon Janar na sojin Isra'ila mai ritaya ya bayyana cewa ɗaya bisa huɗun dakarun wannan runduna ta Golani Brigade sun yi mushe a hannun mayaƙan Palasɗinawa.


Qassam Brigade dai tayi ta sakin bidiyoyi dake nuna yadda suka riƙa yi ma dakarun Isra'ila kwanton ɓauna a kusan kowace rana, wanda a bidiyoyin ana iya ganin yadda mayaƙan na Palasɗinawa ke sarrafa manyan makamai tun daga missiles, bindugun ɗauki ɗai ɗai (Snipers) da kuma yadda suke fasa ta koki, motocin rusau da RPG.


A ranar juma'a  22 ga watan nan na December kafar yaɗa labarai ta Washington Post ta wallafa shaidu daga bakin sojojin Isra'ila dake tabbatar da yadda suka riƙa afkawa tarkon mayaƙan Palasɗinawa.


Ɗaya daga cikin tarkon kuwa shine yadda suka yi amfani da Lasifika (Loudspeaker) inda aka saka mutane na yin magana da Yaren Hebrew na Isra'ila, wanda hakan yasa suka yi tunanin mutanen su ne dake tsare a hannun Hamas.


Abun damuwa dangane da wannan sabon shafi da Isra'ila ke shirin buɗe wa shine cigaba da kai hare hare ta sama zai ƙara sabbaba mutuwar fararen hula.


Zuwa yanzu dai ɓarnar da Isra'ila tayi a Gaza ta zarce ta birnin Aleppo na ƙasar Syria a tsakanin 2012 zuwa 2016, ko Mariupol ta Ukraine, harma hare haren da aka kai Germany a lokacin yaƙin duniya na biyu kamar yadda kafar yaɗa labarai ta AP ta wallafa a ranar 21 ga December.


Ƙasa da fararen hula 355 ke mutuwa a kowace rana, kuma kaso 70 ƙananan yara ne da mata.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments