Daga Yusuf Kabir.
kabiruyusuf533@gmail.com
Da safiyar ranar Litinin 25/12/2023 wakilan 'yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na garin Samaru Zariya,suka ziyarci Chocin TJ.JOSEPH CHATHOLIC Samaru,domin taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti na bana.
Bayan isar tawagar, ta sami tarba daga masu kula da bikin a yayin da aka musu ison shiga da ba su damar gabatar da dalilin ziyarar ta su.Malam Jamilu Habibu Basawa ma'aikaci a NARICT,Zariya ne ya yi bayanin dalilin ziyarar cikin harshen Nasara;Sannan ya mika abun magana ga Husaini Imam Mansur ya gabatar da tawagar da suka kai ziyarar.Bayan haka, sai aka mika abun magana ga Farfesa Isa Hasan Mshelgaru (ABU ZARIYA) domin yin bayanin hadafin ziyarar a dunkule.Shehin Malamin Jami'ar,ya bayyana dalilin ziyarar cikin harshen nasara a yayin da bayyana cewa:''Mun zo ne domin taya ku murnar haihuwar wannan bawa na Allah wanda shi da Mahaifiyarsa sun kasance ayoyi na Allah a cikin halittarsa.''A wani wajen kuma yace:''Hakika addinin Musulunci da addinin Kiristanci dukkaninsu suna da alaka da juna,kuma mabiyansu su ne galiban mutanen da ke rayuwa a Nijeriya.''A yayin da ya juya kan bayanin su maziyartan nan kuma cewa ya yi:"mu Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'qoub Zakzaky (h) ne.A wajenmu dukkanin mutane abun girmamawa ne domin ko dai 'yan uwanmu a addini ne,ko kuma 'yan uwanmu a halitta.''Prof.Mshelgaru ya bayyana cewa:"Sun shekara 25 su na kai irin wannan ziyarar ga Chocina mabambanta kuma hakan yana da matukar amfani.Bugu da kari hanya ce ta kusantar ma'abuta addinan biyu da samar da zaman lafiya da juna.''
Bayan kammala jawabin Farfesa Isa,sai aka gabatar da Fitaccen mawakin Harkar Musulunci Mal.Ammar Dantinka Zariya ya rero dadadan baituka ga Annabi Isah Almasihu (as) a yayin da makadan Chocin suka kida gangunansu domin karawa wakar armashi.
Bayan kammala waken,an gabatar da Dr.Salisu Ahmad Malami a Jami'ar Umaru Musa 'Yar Aduwa domin ya kaddamar da kyautukan da maziyartan suka kaiwa masu hidimar bikin,a yayin da Faston Chocin da dansa suka karba cikin farin ciki da annashuwa.Bugu da kari,bayan hakan sai aka mika abun magana ga Malam Jamilu Habibu Basawa,a yayin da ya gayyato Faston Chochin hade da Farfesa Isa Hasan Mshelgaru,Dr.Salisu Ahmad,Alhaji Mansur Ali,Ammar Dantinka suka yanka Alkaki.cikin farin ciki da annashuwa.
Bayan kammala hakan,daya daga cikin jigogin Chochin ya yi bayanin godiya,a yayin da ya mika abun magana ga Fasto ya yi bayani mai ratsa jiki da nuna jin dadi ga ziyarar da 'Yan uwa Musulmi suka gabatar,a yayin da ya bayyana jin dadin karramawar da aka musu ciki kuwa har da yanka Alkaki.
Wani abun da wakilinmu ya lura da shi da ya karawa ziyarar armashi shi ne;Gayyatar wakilan kafafen yada labarai daban daban da aka yi domin su dauki rahotannin ziyarar tattare da watsawa cikin al'umma.Bello Hamza Editan Jaridar leadership,Mustapha Yawuri daga kafar NAN (tare da tawagarsa),Sagir Hunkuyi daga NTA,Yusuf Kabir daga Jaridar Almizan na cikin 'Yan Jaridar da suka rufawa tawagar baya.
A bangaren 'Yan uwa Musulmi kuwa,tawagar ta su na karkashin Farfesa Isa Hasan Mshelgaru,a yayin da Dr.Salisu Ahamad,Muhammad Barau (Amir din 'yan uwa na Samaru),Alhaji Mansur Ali Samaru,Murtala Bomo,Sagir Yakubu,Mujahid Ahmad,Jamilu Habibu,Ammar Dantinka,Abdurrahaman Musa,Yahaya Abubakar,Mustapha Tukur Galadima,Abduljalal Murtala,Sulaiman Mahmud,Murjanatu Usman,Khadijat Yusuf,Nusaibat AbdulAzeez,Imam Husain Mansur suka mara musu baya.
Wadanda aka kaiwa ziyarar sun nu na matukar farin cikinsu a kan ziyarar,tattare da yin tafi da guda a yayin da maziyartan ke gabatar da bayanai da kuma waka.
Ziyarar dai an fara ta lafiya,an kammala lafiya.
0 Comments