SABON GARGAƊI DAGA YEMEN: Idan Har Isra'ila Ba Ta Dakatar Da Hare Hare A Gaza Ba, Zamu Faɗaɗa Namu Hare Haren - Cewar Janar Mohammed Nasser Al-atifi

 


✍️ Mahadi Tukur Almizan.

Ministan tsaron gwamnatin ƙasar Yemen Janar Mohammed Nasser Al-atifi ya sanar cewa gamayyar rundunonin tsaro masu ɗauke da makamai na ƙasar Yemen za su faɗaɗa hare haren su indai har haramtacciyar ƙasar Isra'ila ba ta kawo ƙarshen kai hare hare Gaza ba.

" Madamar Isra'ila ba ta dakatar da kai hari Gaza ba da dukkanin wuraren da suke kaima hari a yankin Palasɗinu ba, lallai dakarun mu za su ƙaddamar da wasu sabbin Operation fiye da wanda suka yi a baya, cewar Al-atifi a ranar juma'a da dare.

Mujahidan na Yemen dai sun ƙaddamar da hare hare kaitsaye zuwa Isra'ila sannan kuma sun kama manyan jiragen dakon kaya na Isra'ila da masu alaƙa da Isra'ila a cikin tekun Red Sea.

Wanda hakan ya saka Amurka ta ƙuduri aniyar ƙaddamar da wata haɗakar dakaru na ƙasashe mabanbanta domin baiwa jiragen Isra'ila kariya a tekun na Red Sea, sai dai zuwa yanzu wannan ƙuduri na Amurka na gamuwa da cikas domin kuwa wasu daga cikin ƙasashe sun janye daga shiga cikin wannan ƙawance.



Al-atifi ya bayyana cewa sun shirya ma wannan yunƙurin na Amurka da wasu ƙawayen ta da suka shiga cikin wannan ƙuduri na Amurka, domin kuwa a ankare muke idanuwan mu a buɗe muna saka ido.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments