✍️ Mahadi Tukur Almizan
Wata Ƙungiyar kare ƴan cin ɗan adam ta buƙaci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta hukunta wasu manyan jami'an Haramtacciyar ƙasar Isra'ila da aikata laifukan yaƙi a Gaza.
Ƙungiyar dake Amurka ta mika jerin sunayen na mutum 40 na manyan kwamandojin Isra'ila a bisa laifukan yaƙi da suka aikata a Gaza wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan aƙalla Palasɗinawa dubu 20.
Ƙungiyar mai suna 'Democracy for the Arab World Now' (Dawn) ƙungiya ce da fitaccen ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi ya kafa kafin a kashe shi.
Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne a ranar Larabar da ta gabata, ƙungiyar tayi kira ga ICC ta yi bincike kuma ta hukunta waɗannan kwamandoji.
A cewar Sarah Leah babbar Daraktar ƙungiyar ta Dawn, waɗannan kwamandoji su ne ke da alhakin shirya wa da ƙaddamar da hare haren da Isra'ila ke kaiwa kan al'ummar Palaɗinawa, na kashe fararen hula.
Daga cikin mutane arba'in ɗin akwai ministan yaƙi na ƙasar ta Isra'ila Yoav Gallant, Ghassan Alian, da kwamandan 215 Artillery Brigade Ehud Bibi da sauran wasu manyan kwamandojin Isra'ila da ƙungiyar ta ce zata cigaba da bayyana sunayen su anan gaba.
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments