An daɗe ana zargin Isra'ila da ɓoye labaran matattu da masu raunuka daga sojojin ta da ke shan azaba hannun mayaƙan Palasɗinawa.
Aƙalla sojoji 10 ne suka baƙunci ƙiyama a ranar asabar ɗin da ta gabata 23 ga watan December, wanda ya cika adadin sojojin da aka kashe masu a wannan satin yakai sojoji 14.
Sojoji biyar daga ɓangaren Engineering Corps da kuma soja mai kula da lafiya sun gamu da ajalin su yayin da mayaƙan Palasɗinawa suka harba masu makamin fasa Tanka a kudancin Gaza, a yayin da wani abun fashe wa ya tashi da wasu sojojin 4.
Jaridar Israel Times ta labarto cewa " Sojojin Isra'ila 10 aka kashe a ranar asabar".
Hakanan kuma sojojin sun sanar da mutuwar wasu sojojin 4 a ranar juma'a 22 ga wata.
Tun daga sanda Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza, Isra'ilar ta tabbatar da mutuwar sojojinta 153 kawai, sai dai kuma rahotannin asibitoci ya nuna adadin ya wuce hakan, kawai dai Isra'ila na ɓoyewa ne.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Arya dake kafar X wato Twitter a da ya nuna yadda dakarun Hamas suka hallaka sojojin Isra'ila a arewa maso gabashin Beit Lahia, kamar yadda kuke gani a ƙasa.
Hakanan ma a wani bidiyon kuma an nuna yadda dakarun SARAYA AL-QUDS suka yi raga raga da wasu motocin sojojin a gabashin birnin Rafah kamar yadda zaku gani a ƙasa.⚡️Saraya Al-Quds (PIJ) published scenes of mortar launches used to smash military vehicles & D9-bulldozers on the eastern axis of the city of Rafah. pic.twitter.com/3kEeKIQzko
— Arya - آریا 🇮🇷 (@AryJeay) December 24, 2023
⚡️Saraya Al-Quds (PIJ) published scenes of mortar launches used to smash military vehicles & D9-bulldozers on the eastern axis of the city of Rafah. pic.twitter.com/3kEeKIQzko
— Arya - آریا 🇮🇷 (@AryJeay) December 24, 2023
0 Comments