Daga - Mahadi Tukur Almizan
A ranar Alhamis kafar yaɗa labarai ta kasar Syria 'SANA' ta labarto cewa anga ayarin motocin ɗaukar mai na Amurka har guda 45 suna jigilar mai yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Arewacin Iraqi da Man da suka sata daga Syria, sun tsallaka zuwa iraƙi ta 'al-Mahmoudia Crossing'.
Rahoton ya nuna cewa Amurka ta sato wannan mai ne daga yankin Al-Jazeera a cikin ƙasar ta Syria.
Amurka dai ta dade da jibge dakarun ta da kayan aikin a Arewa maso gabashin kasar ta Syria, inda fadar tsaron Amurka (Pentagon) ke bada dalilin cewa dakarun na Amurka na zaune ne yankin domin hana wuraren ɗibar man faɗawa hannun ƴan ta'addan wahabiyawa ta 'ISIS/ISIL' .
Hukumar kasar kuwa ta bayyana cewa wadannan dakaru kawai suna zaune ne domin sace albarkatun kasar ciki harda mai da hujjar cewa tsohon Shugaban Amurka Donald Triumph yasha faɗin cewa Dakarun Amurka na ƙasashen Larabawa ne saboda arzikin man su, Triumph yasha faɗin haka a lokuta mabanbanta.
A shekarar 2019 " Muna ajiye man Syria, mu ke da man, man yana cikin tsaro, mun bar dakarun mu ne saboda man".
Manyan ƙasashen duniya ciki har da China da Rasha sun sha yin Allah wadai da wannan aika aikar da Amurka ke yi na sace mai da sauran albarkatun ƙasar ta Syria, kuma sunyi kira da Amurka ta gaggauta wannan sata.
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments