Daga - Mahadi Tukur Almizan
Amurka ta tura gungun Makaman da ta ƙwace mallakin ƙasar Iran zuwa Ukraine a ƙoƙarin da take na cigaba da rura wutar yaƙin dake faruwa tsakanin Rasha da Ukraine kamar yadda US Central Command suka sanar a ranar 9 ga watan Afrilu.
Manyan jami'an tsaron Amurka sun bayyana cewa Amurka ta ƙwace waɗannan makamai ne a hannun dakarun Ansarullah na Yemen a Red Sea.
Makaman da Amurka ta aika zuwa Ukraine a makon da ya gabata sun haɗa da bindigu ƙirar AK-47 sama da 5000, machine guns,sniper rifles,RPG-7s da rounds ɗin harsasai 7.62- millimeter sama da 500,000.
US Central Command sun bayyana cewa "Amurka ta ƙwace ikon wannan makamai ne a ranar 1 ga watan December na shekarar 2023 sakamakon hukuncin kotu akan waɗannan makamai da suka ƙwace na Jamhuriyar Musulunci ta Iran".
"US Central Command ce ta ƙwace wannan makamai tare da taimakon wasu rundunonin tsaro a tsakanin 22 May na shekarar 2021 zuwa 15 February 2023", CENTCOM ɗin sun bayyana cewa IRGC suna ƙoƙarin jigilar waɗannan makamai ne zuwa ga Ansarullah na Yemen.
Kamar yadda suka wallafa anan👇
"Waɗannan makamai zasu wadaci Brigade guda na Ukraine" cewar CENTCOMU.S. Government Transfers Captured Weapons
— U.S. Central Command (@CENTCOM) April 9, 2024
On Apr. 4, 2024, the U.S. government transferred over 5,000 AK-47s, machine guns, sniper rifles, RPG-7s and over 500,000 rounds of 7.62mm ammunition to the Ukrainian armed forces. This constitutes enough materiel to equip one UKR BDE… pic.twitter.com/Ydecq6OFAo
A watan Oktoban shekarar da ta gabata CENTCOM ta bayyana cewa aƙalla sun aika rounds ɗin harsasai 1.1 miliyan na Iran zuwa Ukraine, a daidai lokacin da Amurka ta yi iƙirarin mallake Assault rifles 9,000, 284 machine guns, rocket launchera 194, da kuma anti-tank guided missiles guda 70 duka na Iran.
Yaƙin da ake yi a Ukraine dai ya shiga shekara ta uku kuma Ukraine ɗin na fuskantar matsanancin ƙarancin makamai.
Idan baku manta ba dai a ranar 29 ga watan Match Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa " Da babu Amurka da ba zamu samu gudummawa ba, ba zamu samu air defense, Babu patriot missiles, da bamu samu 155 millimeter artillery rounds ba, a cewar Zelensky da basu samu waɗannan tallafin daga Amurka ba da tuni sunyi Surrender.
0 Comments