Ansarullah Na Yemen Sun Babbake Tankar Ingila Da Missiles, Kuma Sun Harbo Jirgin Amurka MQ-9.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Mai magana da yawun dakarun Ansarullah na Yemen ya bayyana cewa sun ƙaddamar da sabon hari kan Birtaniya da Amurka domin mayar da martanin hare haren su a Yemen.


Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana cewa bangaren sojin ruwa ba Ansarullah sun hari Tankar man Birtaniya (British) a takun Red Sea, ya bayyana haka ne a ranar juma'a.


Ya kuma kara da cewa sun harbi jirgi maras matuƙi (Drone) na Amurka MQ-9 a lardin Sa'ada (Sa'ada Province).


Ya kara da cewa bayan nufin mayar da martanin hare haren Birtaniya da Amurka kan kasar su, wannan hare haren nuna goyon baya ne ga al'ummar Palestine.


Birgediya Janar Yahya Saree ya mika sakon godiya a madadin rundunar ta Yemen ga al'ummar kasar a bisa amsa kiran Sayyid Abdulmalik Badruddin Alhouthi na fito nuna goyon bayan al'ummar Palestinu da kuma goyon bayan da suke nuna wa ga dakarun na Yemen bisa hare haren da suke kaiwa kan Isra'ila, Birtaniya da Amurka a tekun 'Red Sea, Indian Ocean.." kamar yadda Press TV ta wallafa.



Ya kara da cewa dakarun na Yemen za su cigaba da ayyukan su a Red Sea da sauran Arabian Seas da Indian Ocean har sai ƙasashen Yamma sun dakatar da ta'addancin Isra'ila kan al'ummar Palestinu.

Domin samun data mai inganci da rahusa Ku garzaya Playstore ku Application ɗin 👉 Fadakdata

Dakarun na Yemen dai sun ƙaddamar da hare hare kan jiragen dako na Isra'ila da masu alaƙa da su a Red Sea, da Arabian Seas tun bayan 07 October.



Post a Comment

0 Comments