Daga - Mahadi Tukur Almizan
Ɗari ruwan al'ummar jamhuriyar Nijar ne suka yi zanga-zangae neman Amurka ta kwashe sojojin ta daga ƙasar ta Nijar.
In baku manta ba a cikin watan March ne gwamnatin ƙasar ta Nijar ta yanke alaƙar soji da Amurka kamar yadda suka yanke alaka da Faransa a shekara ɗaya da ta gabata.
Ɗaruruwan masu zanga zangar sun fito ne a babban birnin ƙasar ta Nijar suna masu neman Amurka ta gaggauta tattara dakarunta ta bar masu ƙasa.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
Zanga Zangar ta gudana a ranar Asabar a birnin Niamey, masu zanga zangar sun fito ɗauke da tutar Nijar da kuma alluna masu rubutun dake nuna basu bukatar Amurka a ƙasar su.
Kafin juyin mulkin da ya faru a ƙasar Nijar ta kasance tana ƙawance da France da Amurka, a cewar Amurka suna da dakarun 650 dake aiki a Nijar a cikin watan December na shekarar da ta gabata.
Sojojin Amurka a Nijar suna sarrafa sansanin Amurka dake birnin Agadez wadda ke da tazarar kilomita 920 daga babban birnin ƙasar Niamey, suna amfani da wannan sansani ne wajen tattara bayanan sirri.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
Wannan sansani ne na jirage marasa matuƙi Air Base 201, Amurka ta kashe zunzurutun kudi har kimanin dalar Amurka miliyan ɗari $100m.
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments