Daga - Mahadi Tukur Almizan
Amurka dai ta amince zata janye dakarun ta ne daga Nijar biyo bayan sabon ƙawance tsakanin Nijar ɗin da Rasha.
A ranar juma'a wata jaridar Amurka ta labarto cewa gwamnatin Amurka ta amince zata kwashe dakarunta 1,000 daga Nijar.
Mataimakin Sakataren Amurka Kurt Campbell da Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine sun tattauna a ranar juma'a a shirye shiryen Amurka na fara kwashe sojinta daga Nijar ɗin.
Amurka dai ta mallaki sansanin jiragen tattara bayanan sirri masu matuƙi da marasa matuƙa, da ta kashe kimanin dalar Amurka $100 wajen ginawa a shekarar 2018, sansanin yana nisan kilomita 920km da Miles 572 daga babban birnin ƙasar, ana kiran wannan sansani da Airbase 201.
Sojojin na Amurka dai na zaune ne a Nijar bisa hujjar taimakawa wajen yaƙar ƴan ta'adda a yankin Sahel.
Tun a shekarar da ta gabata General James Hecker na Amurka ya bayyana cewa suna kan neman inda zasu ajiye jiragen su a yammacin Afirka bayan tashi daga Nijar.
Tashar Talabijin din kasar ta Nijar ta kawo rahoto cewa jami'an gwamnatin Amurka za su kawo ziyara Nijar ɗin mako mai zuwa.
A halin yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga dangane da kwashe dakarun kuma babu wani tsayayyen lokacin fara jigilar dakarun.
Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
A cikin watan March ne Nijar ta bada sanarwar yanke yarjejeniyar soji dake tsakanin ta da Amurka ne a watan March da ya gabata, inda Nijar ɗin ta bayyana cewa babu sauran alaƙar soji tsakanin su kuma zata matsa wajen ganin Sojojin Amurka sun bar kasar.
A gefe guda su ma al'ummar kasar sun gudanar da zanga zanga a babban birnin ƙasar suna masu neman Amurka ta kwashe sojojin nata.
Kamar dai sauran ƙawayenta Mali, Burkina Faso Nijar ita ma tayi nasarar korar dakarun kasashen Yamma daga kasar.
Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Dukkanin ƙasashen nan uku, Nijar, Mali da Burkina Faso sun juya ƙawancen su zuwa Rasha, hakanan kuma Rasha a farkon watan nan ta aika da masu sojoji masu bada horo da makaman tsaron sararin samaniya da ake kira "Air Defence System" ƙirar Rasha da wasu kayan aikin Soji zuwa Nijar.
0 Comments