Duniyar Raunana Na Ɓukatar Ire-iren Emad Mugniyeh Domin Lakace Hancin Azzalumai

 


Ya gasa ma Amurka, Isra'ila, Faransa... Aya a hannu, shi suke kira Bin Laden ɗin shi'a a Isra'ila ,  a Amurka kuwa shi ake kira Babban Makashi. 

Emad mugniyeh ya kaddamar da wasu gawurtattun hare - hare guda uku a shekarar 1982, inda ya fara da  bombing ɗin American Embassy dake Beirut a watan Aprilun shekarar 1983, Wanda harin yayi sanadiyyar mutuwar Amurkawa 63, sannan kuma yayi bombing U.S. Marine headquarters duk a Beirut babban birnin ƙasar Lebanon, wanda shima wannan harin ya yi sanadiyyar mutuwar Amurkawa 241, hari na ukun kuwa shine  bombing military camp Na France a yankin Al-Baqa wanda yayi sanadiyyar mutuwar Faransawa 58. 

Hakanan kuma Isra'ila ta tuhumi Haj. Emad da ƙwamushe wasu sojojin Isra'ila a lokacin yaƙin Lebanon. 

A Amurka sunyi Imanin cewa ba a taɓa samun wanda ya kashe Amurka wa da yawa ba kamar shi kafin harin September 11 na shekarar 2001. 

Har sai da ta kai ga Amurka ta saka zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 25 ga duk wanda ya kama mata Haj. Emad, wannan yasa ƙasashe 42 a faɗin Duniya suka yi  kokarin kama shi. 

Kaɗan Daga Tarihin Shaheed Emad Mugniyeh. 

Sunan shi Emad mugniyeh, an haife shi ne a watan January 1962 a garin Soor. 

Shaheed Emad ya kaddamar da ayyukan yaƙar sahayuniyawa a faɗin duniya, sannan yana daga cikin manyan waddanda suka yaƙi ta'addanci da ƴan ta'adda. 

Danginahi duk Sunyi shahada. 

Yayi Karatu ne a American University of Beirut (AUB), Shahid mugniyeh yayi joining forces 17 Na kungiyar Ƴanto Palestine dake Lebanon inda yayi aiki a bangaren safarar makamai a ƙungiyar ta ( Movement of Liberation of Palestine for the Islamic Resistance) Wanda ya taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar Hizbollah da Kuma Amal movement. 

Sakamakon neman shi da hukumomin  Amurka da na Sahayuniyawa ke yi  ne yasa ya ɓuya baya fitowa Media, wannan yasa ya ke da sunaye mabanbanta, Sayyid Hassan Nasrallah yana kiran shi da  Haj. Ahmad. 

Amurka na kiranshi  da babban makashi ( Biggest Killer) 

Su kuwa Sahayuniyawa na kiran shi da Bin Laden ɗin shi'a ( Bin Laden of Shias) 

Saboda ƙwarewar Haj. Emad mugniyeh wajen tsarawa  da Jagorantar  hare hare wannan yasa aka bashi aikin kula da ayyuka (Operations) a ƙungiyar Hizbollah.

Wannan babban gwarzo kuma haziƙi yayi Shahada ne a ranar 12 ga watan February a shekarar 1986, a inda akayi bombing Motar da yake ciki a birnin Damascus wato babban birnin Syria, Wanda yayi sanadiyyar shahadar shi. 

Wanda shahadar shi ta girgiza ƴan gwagwarmaya a Palestine, Hizbullah da ma sauran al'ummar musulmi Na duniya baki daya. 

Amincin Allah ya tabbata a Gare ka ya Shahid Emad Mugniyeh, ranar da aka haife ka, Da ranar da aka kashe ka, Da ranar da za'a tashe ka kana rayayye kuma mazlumi. 

Zehra Kamal | Mahadi Tukur Almizan

   - SHUHADA MADUBINMU - 


©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments