Harin Da Iran Ta Kai Shine Hanya Mafi Kyau Na Hukunta Isra'ila - Cewar Putin

 


Shugaban Iran Ibraheem Ra'isi ya  zantaa ta waya da Putin a ranar 16 ga watan Afril kan al'amarin Faɗaɗar rikicin dake faruwa a gabashin Asiya.


Ra'isi ne ya shirya wannan tattaunawa ta wayar tarho kamar yadda bayanan fadar mulkin Rasha ta bayyana a takardar manema labarai da ta fitar.


Shugabannin biyu sun yi cikakkiyar tattauna daki da daki kan Gabas ta Tsakiya da yunkurin faɗaɗa rikicin da Isra'ila tayi ta hanyar kaima Ofishin jakadancin Iran hari a Syria da kuma martanin da Iran ta mayar.


"Vladimir Putin Yana fatan duka bangarorin biyu zasu dakatar da hare hare kan juna, kar su buɗe sabon filin daga wanda zai haifar da babbar musiba da zata shafi duka yankin" kamar yadda aka wallafa a takardar manema labaran da fadar Kremlin ta fitar.

Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi da rahusa Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata

Ra'isi ya bayyana ma Putin cewa wannan operation na 'True Promise" an tsara shi ne bisa wani kayyadadden hadafi sam Iran bata da niyyar faɗaɗa rikicin a Yankin na Gabas ta Tsakiya.


Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ibraheem Ra'isi ya ƙara jaddada ma takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa Iran zata mayar da martani mafi muni idan ga duk wani hari kan Iran anan gaba.



Daga karshe Ibraheem Ra'isi ya mika godiyar sa ga Shugaba Putin bisa kokarin shi na diflomasiyya wajen kariya ga Iran bayan bayan harin da Isra'ila ta kai mata a Syria.


Saƙon Ra'isi zuwa ga sauran ƙasashen duniya " Gareku kasashen da suka shiga Munafuncin kasashen Yamma masu fuska biyu akan haramtacciyar kasar Isra'ila, kuna nuna damuwar ku kan kada rikicin ya faɗaɗa a yankin Gabas ta Tsakiya, to muna baku shawarar daina goyon bayan kisan kare dangin da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palestinu domin a samu zaman lafiya a wannan yankin".

Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi da rahusa Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata

Rasha dai tayi kokari sosai ta fuskar diflomasiyya daga harin Isra'ila zuwa martanin Iran, domin kuwa bayan Isra'ila ta kai hari Ofishin jakadancin Iran a Syria Shugaba Putin ya fito yayi Allah wadai da wannan harin.


Sannan kuma bayan martanin Iran Putin ya bayyana cewa "Abinda Iran tayi shine martani mafi dacewa tunda dai kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya zama mara amfani".


"Moscow ta tabbata cewa Tehran na daga cikin ginshiƙan zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya". Cewar Putin.


Hakanan wakilin Rasha a majalisar dinkin duniya Vassily Nebenzia ya bayyana cewa lallai martanin Iran na kan daidai, bai faru a baibai ba" yayi wannan zance ne a lokacin zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.


Daga karshen tattaunawar ta wayar, shugabannin kasashen biyu sun yi bayyana kudurin su na cigaba da kyautata alaƙar dake tsakanin su.


A karshe Shugaba Putin ya raya Ra'isi da dukkanin al'ummar musulmi a fadin duniya murnar kammala azumin watan Ramadan da Eidin  karamar Sallah.

Post a Comment

0 Comments