Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Ci Rayukan Mutum 38 A Djibouti

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Aƙalla mutum 38 ne suka mutu sakamakon kifewar   jirgin ruwa a birnin Djibouti cewa hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.


Hukumar ta International Organization for Migration (IOM) ta bayyana cewa wasu mutum 6 kuma sun ɓata suma ƙila sun mutu, akwai kuma wasu mutum 22 da suka tsira daga ibtila'in kifewar jirgin waɗanda jami'an hukumar ta IOM da wasu hukumomin cikin gida suka yi nasarar cetowa.


Mai magana da yawun hukumar ta IOM a yankin Yvonne Ndege ya bayyana cewa jirgin ya kifewa tazarar meter 200 daga Djibouti kuma yana ɗauke da mutanen ne daga Yemen da misalin ƙarfe 2 na dare a ranar 8 ga watan da muke ciki na Afrilu.


Jirgin ya nutse na tsawon awa 2 da mutane 66 akan shi, ana zaton mutanen da jirgin ke ɗauke dasu ƴan ƙasar Habasha ne wato Ethiopia da ƴan Somalia, kuma suna ƙoƙarin tsallaka wa zuwa yankin Gulf a cewar Ndege.


" Sai dai akwai ragowar dubun nan mutanen da suka maƙale a Yemen basu samu tahowa ba, suma dai waɗannan sunyi ƙoƙarin zuwa Djibouti ne domin su ɗan ci lokaci su sake gwada sa'ar tsallakawa ko su koma gida".

Post a Comment

0 Comments