Ƙungiyar ƴan gwagwarmaya ta Lebanon Hezbollah ta bayyana cewa aƙalla Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila 2,000 suka kashe kuma sun raunata aƙalla soji 1,650 tun daga fara yaƙin su da Isra'ila bayan harin "Ɗufaanul-Aqsa" na 07 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.
Hezbollah ta fitar da alƙaluman ne a ranar Laraba da aka cika kwanaki 200 Isra'ila na ta'addanci kan al'ummar Gaza.
Wannan hare haren ta'addanci na Isra'ila sunyi sanadiyyar mutuwar dubunnan Palasɗinawa kuma wasu miliyoyi sun shiga halin ni ƴasu.
Hezbollah ta bayyana alƙaluman hare haren da ta kai kan dakarun sojin Isra'ila wanda suka haɗa da 352 Artillery Shelling, hare haren Drones ta sama guda 54, sun harba Surface to Surface Rockets guda 727, sannan kuma sun harba Guided missiles sannan kuma sun harbi da Machine 77.
A ɓangaren barnar kayayyaki da Hezbollah suka yi ma Isra'ila kuwa ta haɗa da lalata 328 Technical Equipment, 344 bunkers da fortifications, matsugunnan mamaya 722, motocin soji 92, wuraren bada umarni na soji (Command Centers) guda 67, matsugunan Artillery guda 33, Drones guda 5, da kuma Iron Dome missile guda 5, sai kamfanoni 2 mallakin sojin Isra'ila.
Ɗaya daga cikin wuraren da Hezbollah ta yi nasarar Kaima hari yana ɗauke da matsugunai 1,112, yana bakin iyakar Lebanon da Isra'ila.
Hakanan kuma Hezbollah ta lura cewa tayi nasarar korar ƴan kama wuri zaune da Isra'ila ta ƙwaci wuri ta zaunar har mutum dubu ɗari biyu da talatin (230,000) wanda suka koma wasu matsugunai guda 43 masu nisan kilomita 5 daga iyakar ƙasar ta Lebanon da suke zaune kafin fara yaƙin.
Tun bayan harin 7 October da Hamas ta kai Isra'ila yaƙi ya barke tsakanin Hezbollah da Isra'ila a bakin boda.
Kuma Hezbollah taci alwashin cigaba da harar Isra'ila har sai ta daina ta'addancin da take yi a Gaza na kashe raunana.
Wanda yaci rayukan Palasɗinawa 34,305 mafi yawancin su yara da mata ne, da masu raunuka 77,293.
Idan aka koma tarihi za a ga yadda Hezbollah tayi nasara kan Isra'ila a yaƙoƙin da suka taɓa faruwa tsakanin su a shekarar 2000 da kuma 2006.
0 Comments