Daga - Mahadi Tukur Almizan
Tsawon zamani dai jamhuriyar Musulunci na kiyaye fatawar nan ta haramcin mallakar makaman kare dangi wato Nuclear.
Kwamanda mai kula da da muhallan sinadaran nukiliya da basu kariya na kasar Brigadier General Ahmed Haq Talab ya fitar da sanarwa a jiya 18 ga watan Afrilu, sanarwar ta bayyana cewa idan Isra'ila tayi gigin kai hari ɗaya daga cikin muhallan nukiliya na Jamhuriyar Musulunci, to lallai za sauya fatawar haramcin makamin nukiliya.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Ya kara da cewa - "Idan ƴan mamaya suka dauki matakin harar muhallin nukiliya a kasarmu to su shirya fuskantar hari a muhallan nukiliyar su".
"Lallai abu ne mai yiwuwa mu canza dokoki da fatawoyi kan al'amarin nukiliya".
Ya kuma bayyana cewa " Kusan da sanin cewa muna da bayanan dukkanin muhallan nukiliyr ku, kuma hannuwan IRGC na kansu lokaci kawai suke jira su babbakesu da missiles".
Idan kuka yi gigin kawo mana hari to martanin da zaku fuskanta daga dakarun mu zai zamo abun tunawa a tarihi kamar yadda za a rika tuna martanin mu na "True Promise/Wa'adul Haq/Alƙawarin Gaskiya".
Bayanai daga Tel Aviv na nuni da cewa Isra'ila na shirin maida martani a cikin ranakun karshen makon nan (Weekend).
Sai dai rahotanni daga ƙasashen yamma na bayyana cewa Isra'ila zata takaita harin sakamakon matsi daga ƙawayenta.
Duk da labaran karairayi da kasashen Yamma ke yaɗawa na cewa Iran ta mallaki makaman nukiliya tun shekarun 1980s, manyan jami'an jamhuriyar Musulunci sun bayyana cewa wannan labaran karya ne , Iran bata mallaki makaman nukiliya ba saboda fatawar haramcin su da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ɗin Sayyid Ali khamene'i yayi tun shekaru 30 da suka wuce.
Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
"Badan wannan fatawar ba idan muna so mu mallaki makaman nukiliya zamu mallaka kuma baku isa ku hanamu ba kamar yadda baku iya hana mu habbaka makamashin nukiliyar ba, kuma ba zaku iya ba". Cewar Jagora Sayyid Khamene'i a cikin watan June ɗin shekarar 2023.
0 Comments