Daga - Aliyu Dahiru Sufi
Da farko suka ce sun kakkabo jiragen.
Da aka nuna musu bidiyon yadda harin ya yi musu barna a airport din da suke ajiye manyan jiragen yakinsu, sai suka dawo suka ce ai mutum daya ya sama.
Babbar nasarar Iran a yakin nan shi ne, ta fuskanci kariyar kasashe biyar ga harin (Isra'ila, Jordan, Amerika, Faransa da Ingila) amma duk da haka sai da ta yi nasarar samun kasar.
A yanzu Iran ta gano Isra'ila fanko ce wajen cika bakin ko an kai mata hari ba zai yi nasara ba. A yanzu ta gano iya inda karfin bawa Isra'ila kariya yake kuma ta san karfin takanolajinta na kambamawar karya ne.
Don haka yanzu ta bayyana cewa ba batun sake wani sulhu a gaba. Duk ranar da Isra'ila ta ce mata kule sai ta ce cas.
Kuma ka san babbar nasarar? Iran ta kashe kwatankwacin dollar miliyan 65 wajen kai harin. Isra'ila kuwa da kawayenta sun kashe sama sa dollar biliyan daya wajen kare harin. Amma duk da haka sai da aka je inda Isra'ila ke ajiye jiragen yakinta aka babbake.
Wanda bai san ya ake lissafin yaki ba, shi yake zato rushe gini ko kashe sojoji ne nasara kawai. Amma babbar nasara ba ta wuce a gano cika kurinka na karya ba ne ko a gano lagonka. Da haka za a warware maka lissafi.
Shi kuwa Mahmud Labaran Galadanci yayi sharhi ne akan munafuncin siyasar duniya ga sharhin nashi a kasa
Inda zaku tabbatar akwai munafunci a siyasar kasashen duniya musamman western countries shi ne; ita fa Iran ba kirkirar hari tayi ta kaiwa Israel ba. Asali Israel ce ta kaiwa Iran din hari a embassy dinta a Damascus. So, Iran tana martani (response) ne akan abunda Israel tayi mata na barna.
A ka'ida kuma, ana kallon Embassy ne a matsayin kamar kasa duk da baya cikin ainahin kasar. Da aka kaiwa Iran hari a Embassy dinta, hakan yana nuna kasar aka kaiwa hari kai tsaye don Embassy dinta ma kasarta ce.
Amma sabida munafuncin kasashen yamman nan, basu takawa Israel birki ba akan abunda ta yiwa Iran, sai ita Iran din suke yiwa martani. Joe Biden yana ta faman meetings da sauran shugabannin kasashen G7 akan abunda Iran ta yiwa Israel. Su damuwarsu martanin Iran ne, ba wai wadda ta tsokano fadan ba wato Israel.
Ban yi mamakin hakan ba don basu taba tsammanin Iran a shirye take haka ba. Ta rikita su da hare-haren da basu yi tsammani ba. Daga wurare biyar suka rika aika musu kayan aiki ba kakkautawa. Daga Iran, Iraq, Syria, Lebanon da Yemen. Basu yi tsammanin ragargaza haka ba.
0 Comments