Kamfanin Google Ya Kori Ma'aikata 28 Saboda Sun yi Adawa Da Aikin Samar Wa Isra'ila AI Cloud.

 




Daga - Mahadi Tukur Almizan

An sanya wa harƙallar samarwa Isra'ila AI Cloud suna "Project Nimbus", shi dai wannan AI Cloud ɗin zai taimaka ma Isra'ila wajen baiwa bayanan sirri tsaro, wato zai taimaka masu wajen kiyaye bayanai na tsaro, da kuma taimakawa wajen kai hare hare bisa hadafi, gano mutum ta hanyar Facial recognition, wannan yasa ake tunanin Isra'ila tayi amfani da wannan fasaha wajen dauke wasu muhimman mutane a Gaza.


Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta kaddamar da wannan project ne a watan Afrilu na shekarar 2021.


Domin samun Data mai inganci da rahusa Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata

A ranar Laraba 17 ga watan Afrilu da muke ciki ne kamfanin na Google ya kori jimillar ma'aikata 28 wadanda suka yi musharaka a zaman zanga zangar nuna adawa da yin wannan project ga Isra'ila a Ofisoshin kamfanin na Google guda biyu a cikin makon nan.



Ma'aikatan sunyi zanga-zangar ne domin nuna adawa da wannan project wanda zai ci kimanin dala biliyan 1.2 ($1.2) , an kulla wannan harƙalla ne haɗin gwuiwa tsakanin Google da Kamfanin Amazon.

Mai magana da yawun kamfanin na Google ya bayyana cewa hana sauran ma'aikata damar gudanar da aiki da ma'aikatan masu zanga zanga suka yi ya saɓa da dokokin aikin wannan kamfani kuma ba zasu lamunci haka ba, ya bayyana haka ne  da yammacin ranar ta Laraba.

Kamfanin ya shaida ma wasu ma'aikatan da basu yi musharaka a zanga zangar ba kaitsaye cewa an dakatar da su na wani lokaci.

Kafin ranar 17 ga watan, a ranar 16 ga wata kamfanin ya kori ma'aikata 9 kuma ƴan sanda sun kama.

Domin samun Data mai inganci da rahusa Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata

Tun a lokacin da aka ƙaddamar da wannan project dai a shekarar 2021 ɗaruruwan ma'aikata daga kamfanin Google da Amazon  sun nuna adawa da project ɗin harma sun rubuta takarda an wallafa a jaridar "The Guardian" sun rubuta wannan takarda ne domin Amazon da Google su dakatar da wannan project ɗin, sannan kuma su yanke duk wata alaƙa da sojin Isra'ila.


Tun bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da Hamas a October an yi ta samun yawaitar masu adawa da wannan project daga cikin ma'aikatan kamfanonin, ko a cikin watan March na wannan shekarar da ya gabata an kori wani Ma'aikaci wanda yake cewa "Ba zan gina fasahar da zata karfafi kisan kare dangi ba", akan haka ne aka kore shi.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments